Labarai

ƘAREWAR KWANA: Daliget daga Jigawa ya rasu a daidai yana karin kumallo a Abuja

Ɗaya daga cikin Daliget ɗin dake halartar gangamin jam’iyyar APC a Abuja ya yanke jiki ya faɗi a daidai yana kwankwadan shayi da safiyar Talata.

Daliget ɗin mai suna Isah Baba Buji ya rasu ranar Talata.

Kakakin jam’iyyar APC na jihar Jigawa Bashir Kundu ya tabbatar da rasuwar Baba Buji.

” Baba Buji ya rasu da safiyar Talata a lokacin ya na karin kumallo. Yana cikin shan kofin shayi sai kawai ya yanke jiki ya faɗi, ko da aka duba shi ya riga ya yi sallama da duniya.

A karshe Kundu ya ce za a maida gawar sa gida, wato can Jigawa domin ayi masa sutura.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news