Wasanni

ƘUNCIN RAYUWA: Ahmed Musa ya aika wa wani tsohon ɗan kwallon Najeriya kyautar naira miliyan biyu

Kinsley Obiekwu fitaccen ɗan wasan Najeriya a lokacin da Najeriya ta yi ta she da suna wajen yin nasara a wasan kwallon kafa a nahiyar Afrika.

Obiekwu da shi aka yi nasara a wasan kwallon kafan Atalanta 96 wanda Najeriya ta yi ci gwal.

Ɗan wasan ya ce tun bayan dawowarsa Najeriya a 2008 ya faɗa cikin halin ƙaƙanikayi. Ya talauce sannan ga kuma iyali. Karshenta dai ya wuya ta yi wuya sai ya koma direban motan haya.

” Dama ƴar mota ta guda ɗaya ce da nake ɗan gurgurawa, ina da yara huɗu da suke Jami’a, daya na sakandare. Dole na ke yin kabukabu domin in rike su.

Sai dai kuma bayan ya bayyana matsalar sa a yanar gizo sai Kaftin din kungiyar Super Eagles, Ahmed Musa ya aika masa da naira miliyan biyu kyauta domin ya rage zafi.

Obiekwu ya tabbatar da samun alat din naira miliyan biyu da Ahmed Musa ya shiga ka masa da shi.

Wannan ba shi ne karon farko da Ahmed Musa ya ke taimakon mutane musamman marasa ƙarfi a ƙasarnan ba.

Ko a kwanakin baya da suka tafi ƙasar Kamaru wasan cin kofin Afrika, Musa ya tallafa wa wani masallaci da dala 1,500 baya ga wasu da dama da yake yi wa mabuƙata.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. Thanks for finally writing about > ƘUNCIN RAYUWA: Ahmed Musa ya aika wa wani tsohon ɗan kwallon Najeriya kyautar naira miliyan biyu – labarai.haske247.com < Liked it!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news