Labarai

Ƙungiyar IPMAN ta ce ba za ta iya ci gaba da sayar da fetur a garuruwan yankin Igbo ba

Ƙungiyar Masu Hada-hadar Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana cewa ba za su iya ci gaba da lodin fetur ana rarrabawa a cikin garuruwan yankin ƙabilar Igbo ba, wato Kudu maso Gabas a kan farashin da ake sayar da shi a yanzu.

Manyan dillalan man sun tattauna ne da manema labarai a wata tattaunawa daban-daban da aka yi da su a Awka, ranar Juma’a.

Sun ce idan wanda gare su yanzu a ƙasa ya ƙare, to ba za su ci gaba da raba fetur ɗin su na sayarwa ba.

Rahotanni sun nuna a cikin garin Awka ana sayar da fetur lita ɗaya naira 180, wasu gidajen man kuma har 195.

Rahotanni sun tabbatar ana sayar da gas daga naira 850 duk lita ɗaya, wasu wuraren kuwa naira 900 su ke sayar da lita ɗaya.

Wani dilan fetur mai suna Emeka Nnoli, ya shaida cewa su na yin asarar sosai idan su na sayar da litar fetur kan farashin da gwamnati ta ƙayyade.

Nnoli ya ce a yanzu ba su iya samun fetur kai-tsaye daga NNPC kan farashin gwamnati.

“Mun dogara ne da sayen mai daga daffo ɗin ‘yan kasuwa masu tsawwala farashi.”

Sannan kuma ya koka kan yadda ake ci gaba da tsawwala kuɗin jigilar kaya zuwa Kudu maso Gabas.

“Ba zamu iya ci gaba da sayar da fetur a kan farashin da na yanzu ba a yankin Kudu maso Gabas.

“A yanzu farashin fetur a gidajen mai naira 168 duk lita ɗaya. Kuma za mu biya Naira 15 kuɗin lodi, sannan ga kasada da saida rai.”

Idan ka kalli abin za ka ga idan muka sayar da fetur duk lita ɗaya ƙasa da Naira 200, to za mu kwan cikin jarin mu.

An tattauna da masu harkokin fetur da dama, kowa na kawo matsalolin da su ke fuskanta.

Shugaban IPMAN na Jihar Enugu mai suna Chinedu Anyaso, ya bayyana cewa masu sayar da fetur ba za su yarda su yi ta ɗibga asara ba, saboda ba su iya yanka farashin litar fetur.

“A yanzu dai mu na da fetur Anambra, Ebonyi da Enugu. Amma idan wanda ke ƙasa ya ƙare, to ba za mu yi maku alƙawarin samar da fetur ba. Mun gaji da ɗibga asara haka nan.”


Source link

Related Articles

One Comment

  1. I’m extremely impressed along with your writing skills
    and also with the format on your weblog. Is this a paid topic or did you modify it yourself?
    Anyway keep up the nice high quality writing, it’s rare to look a
    great blog like this one nowadays..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news