Labarai

Ƴan bindiga sun saki fasinjojin jirgin Kasa 7

Tukur Mamu ya bayyana cewa ƴan bindiga sun saki ƙarin wasu fasinjojin jirgin kasa da suka yi garkuwa dasu.

Waɗanda aka saki sun haɗa da Muhammad Daiyabu Paki, Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule, Sadiq Ango Abdullahi, Aliyu Usman Muhammad Abuzar Afzal dan asalin kasar Pakistani.

Mamu ya ce sai da suka yi tafiyar kilomita 40 a cikin daji kafin nan suka gamu da sojojin da suka raka su zuwa Kaduna.

Har yanzu akwai sauran fasinjoji tsare a hannun ƴan bindigan wanda ke jiran tsammani.

Fasinjojin sun shafe kwanaki sama da ɗari tsare a hannun ƴan bindiga.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button