Labarai

Ƴan bindiga sun saki fasinjojin Jirgin kasa n Abuja-Kaduna

Ƴan ta’addan da suka sace matafiya a jirgin kasa da ya taso daga a Abuja-Kaduna a watan Maris sun sami ƙarin mutum biyar.

Idan ba a manta ba, ƴan bindigan sun saki wasu daga cikin fasinjoji hudu a makon jiya.

Tukur Mama, wanda shine mawallafin jaridar Desret Herald, kuma wanda yayi suna wajen tattaunawa da ƴan bindigan ya ce waɗanda aka saki sun ziyarce shi a ofishin shi dake Kaduna domin yi masa godiya.

Mamu ya taba cewa ya janye hannun sa daga tattaunawar fafitikar ceto waɗanda aka yi garkuwa da su saboda nuna halin ko in kula daga ɓangaren gwamnati.

Fasinjojin sun shafe samada kwanaki 120 a hannun ƴan bindigan.

Waɗanda aka sake sune, Mustapha Imam, wanda Farfesa ne a jami’ar Usman Danfodio, Akibu Lawal; Abubakar Rufai; Mukthar Shu’aibu; da Sidi Sharif.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. I am really loving the theme/design of your weblog. Do you ever run into any web browser compatibility problems? A number of my blog visitors have complained about my blog not operating correctly in Explorer but looks great in Firefox. Do you have any recommendations to help fix this problem?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button