Nishadi

Ƴan matan Kaduna da Katsina ne ke kan gaba wajen matan da suka fi kwaɗayi a Najeriya – Rahoto

A wani rahoto da wani mai yin bincike da sharhi kan sha’ani na zamantakewa da soyayya, ya nuna cewa ƴan matan da matan aure ƴan jihar Kaduna sun fi sauran matan yankin Arewacin ƙasar nan ƙwaɗayi da sin abin hannun mutane.

Bisa ga wannan rahoto, matan da ke jihar Kaduna sun fi son saurayi ya basu ƙudi da abin hannun sa idan har yana so ya samu damar su su rika sauraran sa.

” Idan a Kaduna kake neman mace ko da aire ne, babban burin ta shine ka zamanto mutum mai kuɗi sannan kuma mai kashe su yadda ya kamata. Cikin Ɗan kankanin lokaci za ka ga suna bin ka kamar ƙudan zuma.

Da yawa daga cikin matan Kaduna sukan fi zaman aure ne idan mazajen su masu hali ne, idan kuwa ba haka ba, kun dinga samun matsala da iyalin ka kenan.

Jiha ta biyu dake bi mata, ita ce jihar Katsina.

Suma ƴan matan jihar Katsina irin wannan tafiya suke yi. Dama kuma ƴan biyu ne masu kama ɗaya.

” A jihar Katsina, sai kana da abin hannu fa. Idan ba haka ba gaskiya rike mace zai yi maka wahala a wannan zamani. Domin muna da ‘taste’” in ji Hindatu Sani.

Jihar Jigawa, Bauchi da Gombe, sune ke can kasa a teburin wanda matan su ba su damu da aljihun ka ba, soyayyace suka fi damuwa da ita.

” Mu a yankin mu idan na miji ya nuna maka tsantsagwaran soyayya, ya ishe mu ba sai ka tara maƙudan ƙudi ba.

Su ko Kanawa kuɗin ka bai dame su ba, idan suna sonka shike nan.

” Ƴan matan Kano sai su yi maka hanyar arziki ma idan har suna ƙaunarka ba sai ka zo musu da buhunan kudi ba.

” Babban abinda suka fi shine mace kyakkyawa fara, burin bakane kenan. Shi dai ace matar sa fara ce tas-tas, son kowa kin wanda ya rasa. ”

Wannan Rahoto na bincike da aka yi a kan wasu bangare na mata dake wasu daga ciki jihohin Arewacin Najeriya.


Source link

Related Articles

5 Comments

 1. Have you ever considered writing an e-book or guest authoring
  on other websites? I have a blog centered on the
  same subjects you discuss and would love to have you share some stories/information. I know my
  subscribers would enjoy your work. If you are even remotely interested, feel free to shoot me an e mail.

 2. Hi, There’s no doubt that your web site may be having browser compatibility problems.
  When I look at your site in Safari, it looks fine however when opening in I.E., it has some overlapping issues.
  I simply wanted to provide you with a quick heads up!
  Apart from that, great website!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news