Nishadi

Ɗan takarar gwamnan Kano AA Zaura zai tallafa wa dalibai ƴan asalin jihar Kano da tallafin kuɗi har naira Miliyan 200

Gidauniyar Ɗan takarar gwamnan jihar Kano AA Zaura Foundation ta sanar da ware wasu har naira miliyan 200 domin tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano dake manywn makarantun kasar nan.

A sanarwar wanda Daily Nigerian ta buga a yanar gizo, Zaura ya ce wannan ɗaya ne daga cikin alƙawurran da yayi a sakon sa na sabuwar shekara da yayi wa mutanen jihar Kano.

” Sanin kowa ne ilimi shine ginshikin zaman duniya, a dalilin haka ne zan tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano 10,000 da tallafin naira 20,000 kowannen su.

” Mun samar da fom din da za a cika zassauƙi ba tare da an wahala ba. Bayan haka kuma akwai tallafi da Gidauniyar AA Zaura zai baiwa mata da kungiyoyi fon cigaban al’umma a jihar Kano.

Bi nan domin samun wannan tallafi: https://aazaura.org.ng/education-support-fund/


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. Pingback: 1interspersed
  2. Pingback: gay on line dating

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button