Labarai

2023: ‘Ba za mu ƙara wa jam’iyyu wa’adin yin zaɓen fidda-gwani ba’ -INEC

Yayin da ake raɗe-raɗin cewa APC na neman alfarma daga INEC domin a ƙara wa jam’iyyu wa’adin rufe ranar yin zaɓen fidda-gwani, sai ga shi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ba za ta ƙara ko da rana ɗaya ba.

A cikin jadawalin da INEC ta fitar na shirye-shiryen zaɓen 2023, hukumar ta ware tun daga ranar 4 Ga Afrilu zuwa 3 Ga Yuni ya kasance tilas kowace jam’iyya ta gudanar da zaɓen fidda-gwani, kuma ta fitar da ɗan takarar kowane muƙami a jiha da ƙasa baki ɗaya.

Ana sauran kwanaki 28 kenan wa’adin fitar da ɗan takara ya cika, APC da PDP sun nuna ba su shirya gudanar da zaɓukan fidda gwani ba.

Yayin da APC har yanzu ta na ci gaba da sayar da fam na takara, ita kuwa PDP yanzu ne ma ta ke tantance waɗanda su ka nuna sha’awar tsayawa takarar.

Sai dai kuma rahotanni na nuni da cewa manyan jam’iyyun biyu su na ta neman kamun-ƙafar INEC domin a ƙara masu lokaci.

Zuwa yanzu dai mutum 23 ya nuna sha’awar takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, sai kuma mutum 17 ke neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa ‘yan takara 15 tuni sun lale Naira miliyan 100 kowanen su ya sayi fam na neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC.

Fiye da rabin mutum 17 masu nema daga PDP duk sun lale Naira miliyan 40 kowanen su ya sayi fam ɗin.

Yayin da APC ke sayar da na ta dam ɗin naira miliyan 100, ita kuwa PDP Naira miliyan 40 ne farashin na ta fam ɗin na takarar shugaban ƙasa.

Kakakin Yaɗa Labaran da kuma wayar da kai na INEC, Festus Okoye, ya gargaɗi jam’iyyu kada su kuskura su yi wa ƙa’idojin da INEC ta gindaya riƙon-sakainar-kashi.

“Ganin irin yadda zaɓen fidda-gwani ke da muhimmanci wajen fitar da ‘yan takara a zaɓukan 2023, to akwai buƙatar mu sake nanata wa jam’iyyun cewa sauran kwanakin da su ka rage domin su fitar da ‘yan takara bai kai wata ɗaya cur ba. Za a rufe karɓar sunayen ‘yan takara a ranar 3 Ga Yuni, 2023.”


Source link

Related Articles

7 Comments

 1. Pretty section of content. I just stumbled upon your blog and
  in accession capital to assert that I acquire in fact enjoyed account your blog posts.
  Anyway I’ll be subscribing to your feeds and
  even I achievement you access consistently fast.

  Feel free to surf to my web-site cash game

 2. I like the valuable info you provide in your
  articles. I’ll bookmark your weblog and check again here regularly.
  I am quite sure I will learn lots of new stuff right here!
  Good luck for the next!

 3. Göbekli Cami Halısı Göbekli cami halısı halının orta yerinde büyükçe bir motif bulunan cami halıları modellerindendir. Bu modelin ortasındaki motifinin kenar kısımları ise düzdür. Göbekli cami halısı, zarif ve estetik bir görünüm sunar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button