Labarai

2023: Dalilin da ya sa muka shawarci Tinubu ya ɗauki Musulmi mataimakin takara -Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa idan ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa, zai ɗinke ɓaraka da kuma ƙara haɗa kan ƙabilu da mabiya addinai daban-daban a ƙasar nan.

Ganduje ya ce shugabannin APC ne su ka haɗu su ka shawarci Tinubu ya ɗauki Musulmi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ba don komai ba, sai domin a kawar da tsoro da shakkun da mabiya addinai ke wa ɓangarorin su.

Ganduje ya shaida wa BBC Hausa haka a ranar Juma’a, yayin da ya kai ziyarar taya APC kamfen ɗin takarar gwamnan Jihar Osun takarar zaɓen gwamna da za a yi.

Ganduje ya ce APC ta yanke shawarar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa Musulmi da kuma mataimakin takara Musulmi, domin a kawar da ninancin da ake sakawa ta fuskar addini a siyasa ko a mulkin Najeriya.

“Mu ne muka shawarci Tinubu ya ɗauki Musulmi mataimakin takarar sa, domin daga yanzu a kawar da bambancin addinin ta ya yi wa ƙasar nan katutu a tsarin siyasar ta.

“Gara tun yanzu mu tashi mu kawar da duk wani abin da ke kawo mana rabuwar kawuna, domin haɗin kan da za mu tabbatar ya amfane mu a gaba.”

Ganduje ya ce idan har ba a kawar da fifita addinin da mutum ya ke maimakon a nemi cancanta ba, to matsalar za ta yi ta addabar mu nan gaba.

Gwamnan na Kano ya ce Tinubu zai zama shugaban kowa da kowa a Najeriya, ba shugaban wani addini ko na wata ƙabila ita kaɗai ba.

Tun bayan da Tinubu ya bayyana sunan Kashim Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ya ke shan suka daga ɓangaren Kiristoci da kuma manya da ƙananan ‘yan APC.

Bayyana sunan Kashim Shettima ya tayar da ƙura da hayaƙi, har ta kai ga Fadar Shugaban Ƙasa ta yi sanarwar cewa babu wani rahoton SSS kan takarar Tinubu-Shettima da aka aika wa Buhari.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da wata jarida ta buga, inda ta ce Hukumar Tsaro ta SSS ta aika wa Shugaba Muhammadu Buhari rahoton shawarwari dangane da batun ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Bola Tinubu a jam’iyyar APC.

Garba Shehu, Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari ne ya fitar da sanarwar a ranar Juma’a, inda ya shawarci ‘yan Najeriya cewa su yi watsi da labarin, duk ƙarya ce tsagwaron ta kawai.

Duk da cewa Garba Shehu bai ambaci sunan jaridar ba, amma dai a ranar Laraba jaridar Peoples Gazette ta wallafa cewa wai Hukumar SSS ta yi gargaɗin cewa “takarar Musulmi shugaba kuma Musulmi mataimakin sa, za ta iya hargitsa Najeriya.”

Jaridar ta ce ta samu bayanin ce ƙunshe a cikin wasu bayanan sirri da aka gulmata mata, sai kuma hirarrakin da ta ce ta yi da wasu jami’an leƙen asiri.

A raddin da mayar, Garba Shehu ya shawarci “duk wani wanda ya san ya kamata mai hankali, ya yi watsi da labarin, abin dariya ne kawai wata jaridar yanar zigo ta rubuta wa jama’a shifcin-gizo, domin kawai ta haddada rabuwar kawuna, kuma ta kawo ruɗani a kan zaɓen da ɗan takarar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi wa tsohon Gwamna Kashin Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.”

Idan ba a manta ba, bayan Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ya ce ya ɗauke shi ne ba saboda addinin su ɗaya ba, sai don cancantar sa kawai.

Tinubu ya ce duk da ya san akwai damuwa daga wani ɓangare, saboda zaɓen mataimakin sa Musulmi, tunda shi ma Musulmi ne, amma dai bai yarda cewa batun addini ne zai zama abu mafi cancanta wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ba.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news