Labarai

2023: GARGAƊIN BUHARI GA HASALALLUN APC: Ku daina saka ni cikin hauragiyar ku

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa sai ɗan takarar da APC ta tsayar kaɗai zai goya wa baya a zaɓukan 2023, a matakai daban-daban na zaɓen.

Buhari ya ce ba zai goyi bayan duk wani fanɗararren ɗan APC da ya fusata don ya faɗi zaɓen fidda-gwani ya koma wata jam’iyya ba, ko kuma wanda ya garzaya kotu ya hana APC sakat.

Waɗannan bayanai su na cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya fitar, ranar Laraba a Abuja.

Buhari ya ce duk wanda ya fice daga jam’iyya ko ya garzaya kotu saboda bai yi nasara a zaɓen fidda gwani ba, to ya je can ya ƙarata. Waɗanda ke cikin wata jam’iyya kuma su daina danganta abin da su ke yi da Buhari, don kawai sun fice daga APC.

“Fadar Shugaban Ƙasa na jan hankali ga dukkan ‘yan APC na haƙiƙa.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news