Labarai

2023: Gwamnoni ke rura hargitsi da tarzomar siyasa – Sufeto Janar na ‘Yan Sanda

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya fito ƙiri-ƙiri ya bayyana cewa rikice-rikicen siyasar da ke ci gaba da faruwa a wasu jihohi duk laifin gwamnonin jihohin ne.

Baba ya ɗora wa gwamnoni wannan laifi a lokacin da ya gayyaci jam’iyyun da su ka fito takara domin ganawa da su kan gargaɗi da tattauna hanyoyin daƙile rikice-rikicen siyasa kafin zaɓen 2023.

A taron wanda ya yi da jam’iyyun da wasu masu ruwa da tsaki, Sufeto Janar Baba ya ce gwamnoni na amfani da wasu jami’an tsaron da jihohi su ka kafa su na cin zarafin jam’iyyun adawa ko ‘yan adawar.

Ya ce karya doka ce a hana wata jam’iyya yin amfani da wasu wurare domin gudanar da tarukan su na siyasa, wanda doka ba ta haramta ba.

Ya ce gwamnoni su na ɗaure wa manyan ‘yan siyasa gindi, su kuma su na amfani da masu tayar da fitina kan ‘yan adawa.

“Daga cikin abin da gwamnonin ke wa masu adawa, akwai hana su amfani da wuraren taro, cinna masu ‘yan bangar siyasa ɗauke da makamai, yagewa da kekketa masu fastocin ‘yan takarar su da yin amfani da ƙarfin jami’an tsaron sa-kai waɗanda jihohi su ka kafa su na tarwatsa tarukan ‘yan adawa.

Cikin makon jiya ne Mashawarcin Shugaba Buhari kar Harkokin Tsaro ya bayyana cewa cikin kwanaki 30 an samu rahotannin hargitsin siyasa sau 52 cikin jihohi 22.

Haka nan a farkon wannan makon Babban Limamin Katolika na Jos, Mathew Hassan Kukah ya ce duk jihar da rikicin siyasa ya tashi laifin gwamnoni ne.

Babban Limamin Ɗariƙar Cocin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, ya yi kira ga ‘yan Najeriya cewa su ɗora laifin ɓarkewar rikice-rikicen siyasa a kan gwamnonin jihohi.

Ya ce akasari duk rikicin siyasar da ya tashi da wanda zai tashi kafin nan da zaɓen 2023, duk gwamnonin jihohi ne musabbabin su.

Kukah ya yi wannan tsokaci a cikin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya yi da shi a ranar Talata.

Ya ce wasu gwamnonin jihohi ƙiri-ƙiri su na hana jam’iyyun siyasa yin amfani wuraren taruka mallakar jihohi, lamarin da faston ya ce hakan na haifar da rikicin siyasa a jihohi daban-daban.

Wannan bayani na Kukah ya zo kwanaki huɗu bayan Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari kan tsaro, Babagana Monguno ya bayyana cewa a cikin kwanaki 30 bayan fara kamfen, an samu tashe-tashen hankula a wurare 52 cikin jihohi 22.

“Ni ina ganin cewa gwamnoni sun fi sauran rukunan ‘yan Najeriya laifin haddasa ɓarkewar tashe-tashen hankula. Saboda su ne masu wuƙa da naman da ke riƙe da wasu wuraren da dalilin su rikicin ke yawan tashi,” inji Kukah.

Ya ce sannan kuma wasu gwamnonin da su ka canja sheƙa zuwa wata jam’iyyar na haddasa rikici ta hanyar ƙoƙarin tirsasa wa sauran jami’an gwamnati bin su zuwa jam”iyyar da su gwamnonin su ka koma.

“Kuma abin takaici ne yadda waɗannan gwamnoni ke nuna kamar ba su da masaniyar cewa magoya bayan su na kekketa fastar jam’iyyun adawa.”

Ya ce abin damuwa ne matuƙa yadda waɗannan gwamnoni ba su ɗaukar darasi daga kura-kuren da su ka tafka a baya, wanda ya yi sanadiyyar ɓarkewar tarzomar siyasa.

Da ya ke bada misalin halayyar ‘yan siyasa da wani bidiyon da aka nuno Atiku Abubakar da Bola Tinubu zaune a filin jirgi su na raha da annashuwa, Kukah ya ce hakan darasi ne da ya kamata talaka ya ɗauka cewa su fa ‘yan siyasa duk ‘dodo ɗaya su ke wa tsafi’, wato dukkan su abokan juna ne masu tseren rige-rigen kaiwa ga dukiyar al’umma kawai.

A kan haka sai ya ja hankalin jama’a cewa su guji nuna wa ‘yan siyasa makauniyar soyayya, domin duk yadda ‘yan siyasa ke gaba ko adawa, wata rana tare za ka gan su, wuri ɗaya kuma a jam’iyya ɗaya.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button