Labarai

2023: Kada ku kuskura ku zaɓi waɗanda za su kashe ku -Gargaɗin Jonathan ga matasa

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya gargaɗi matasa da sauran ‘yan Najeriya cewa kada su kuskura su zaɓi masu kashe su idan zaɓen 2023 ya zo.

Jonathan ya yi wannan gargaɗin ne a taron murnar cikar Jihar Akwa Ibom shekaru 35 da ƙirƙirowa. An yi taron a Uyo babban birnin jihar a ranar Lahadi.

Jonathan da matar sa Patience ne manyan baƙi na musamman a wurin taron addu’ar, wanda shi ma Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa ya halarta.

“Idan zaɓen 2023 ya zo, kada ku kuskura ku yi gangancin zaɓen masu kashe ku.

“Masu ɗaukar takubba, wuƙaƙe, bindigogi su na kashe mutane saboda siyasa, su ne maƙiya al’umma.

“Idan ka kashe mutane ka zama shugaba, to za ka ci gaba da kashe mutane domin ka ci gaba da zama kan shugabancin. Kenan mutane ne za su ci gaba da shan azaba a ƙarƙashin ka.”

Jonathan ya ce tun wajen 1994 ya fara lura da irin ci gaban da Jihar Akwa Ibom ke samu sannu a hankali, lokacin da ya zama mataimakin darakta a hukumar raya yankin Neja Delta. Ya ce ya kan je Akwa Ibom aƙalla sau ɗaya a shekara.

Ya gode wa matasan jihar Akwa Ibom saboda ba su ɗauki mummunar ɗabi’ar lalata kayan gwamnati ba.

Jonathan ya tunatar da yadda wasu marasa kishin ƙasa su ka riƙa sa zarto su na yanke kayan wutar lantarki a zamanin sa, saboda kawai su na so Najeriya ta ci gaba da kasancewa cikin duhu.

Jonathan ya ce zaɓen da ‘yan Jihar su ka yi wa Gwamna Emmanual Udom zai kasance darasi ga ‘yan siyasa, musamman ga waɗanda kafin zaɓen su ka riƙa shakku da tababar cancantar sa wajen iya tafiyar da mulkin jama’a.

Kafin Udom Emmanuel ya zama Sakataren Gwamnatin Akwa Ibom, babban darakta ne a Zenith Bank.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button