Labarai

2023: Tinubu ya sha alwashin ci gaba da ayyukan raya ƙasar da Gwamnatin Buhari ta gina

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya sake jaddada alwashin cewa idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa a 2023, to zai ,ci gaba da ayyukan raya ƙasa daga inda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya.

Tinubu ya sha wannan alwashin ne lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Nazari da Bitar Ayyukan Ministoci a ranar Talata, a Abuja.

Tinubu ya je wurin taron ne bisa gayyatar musamman da masu shirya taron su ka yi masa, inda a wurin ya jinjina wa Buhari “saboda ya yi ƙoƙari ƙwarai” wajen samar da ayyukan raya ƙasa tun daga lokacin da ya zama shugaba a 2015.

“Ya Shugaban Ƙasa, ina roƙon kai da Ministocin ka ku ji wannan bayani daga baki na, idan aka zaɓe ni zan ba ka martaba da daraja ta hanyar ci gaba da ayyukan alherin da ka yi

“Zan yi aiki tuƙuru domin ƙara danƙon haɗin kai a ƙasar nan, kamar yadda jam’iyyar da ke kan wannan tunani da aiwatarwa a ƙarƙashin gwamnatin ka.

Tinubu ya jinjina wa irin ƙoƙarin da Buhari ya yi tun daga farkon hawan sa mulki, a lokacin da ƙasar nan ke fama da matsanancin ƙalubale.

“Ka shiga ofis daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke kafa tutuci a wasu yankunan ƙasar mu, su na ayyuka haramtacciyar jihar su. Amma a yanzu saboda ƙoƙari da jajircewar ka, duk babu sauran wannan barazanar a yanzu.

A jawabin sa na Kaduna kuwa, Tinubu ya ce zai jajirce na kawar da ‘yan bindiga, na bunƙasa noma da inganta fannin ilmi.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu, ya tabbatar da cewa zai yi iyakar dukkan abin da ya wajaba domin ya kakkaɓe barazanar rashin tsaro, musamman ‘yan bindiga a ƙasar nan.

A janwabin sa wurin Taron Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa, a ranar Litinin a Kaduna, Tinubu ya ce “zan yi amfani da duk abin da gwamnati na ya wajaba ta yi amfani da shi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Taron wanda aka gudanar, Tinubu ya ce shi ba baƙon zuwa Arewa House ba ne, domin ko shekarar da ta gabata, shi ne Shugaban Lakcar Tunawa da Sardauna.

“Ni ba baƙo ba ne a wannan wuri, na sha zuwa lakca, domin ko shekarar da ta gabata ni ne Shugaban Lakcar Tunawa da Sardauna.

“Zuwa wurin nan ya na tuna mana manya ‘yan kishin ƙasa da kishin al’umma irin su Sa Ahmadu Bello Sardauna, wanda ya gina al’umma kuma ya gina cibiyoyin ilmi.”

Da ya ke magana kan matsalar tsaro musamman ‘yan bindiga, Tinubu ya ce zai yi irin abin da ya yi har ya wanzar da tsaro a jihar Legas, a lokacin da ya zama gwamna a 1999.

“Lokacin da na zama Gwamna cikin 1999, na samu Legas hannun ‘yan bindigar cikin birane, waɗanda su ka mamaye yawancin titina, sai yadda su ka ga dama su ke yi, wajen aikata munanan laifuka.

“Amma mun shigo da tsare-tsaren da mu ka kakkaɓe ɓatagari, har ta kai Legas ta zama son kowa, ƙin wanda ya rasa samu.

“Saboda haka za mu bi ƙasar nan mu samar da irin tsaron da muka samar wa Legas, ta yadda kowane wuri zai zama abin sha’awa mai cike da tsaro da zaman lafiya.”

Tinubu ya ce idan ya yi nasara, gwamnatin sa za ta rugurguje duk wasu masu neman hargitsa Najeriya.

Da ya taɓo tattalin arzikin ƙasa kuwa, Tinubu ya ce za a inganta tsarin zuba jari, maida hankali wajen bunƙasa noma, inganta tattalin arzikin fasahar zamani, kuma gwamnatin sa za ta mara wa masu masana’antu ta yadda za a bunƙasa su, sannan a farfaɗo da waɗanda su ka durƙushe.

Jagaban na Borgu ya ce gwamnatin sa za ta samar da aikin yi ga ‘yan Najeriya, za ta inganta wutar lantarki, albarkatun ƙarƙashin ƙasa, fannin ilmi, kuma za ta magance yawan gararambar da yara ke yi marasa samun galihun zuwa makaranta.


Source link

Related Articles

6 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button