Labarai

2023: Zaɓe ba shi da wani amfani, matsawar sai an je kotu ake tabbatar da shugabanni – Lauya Adegboruwa

Wani lauya mai suna Ebun-Olu Adegboruwa, ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda kotuna ke yawan soke zaɓukan fidda-gwanin jam’iyya, ko da kuwa bayan zaɓe na game gari. Kuma ya damu da yadda kotunan ke yawan tsige waɗanda aka zaɓa.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, Adegboruwa ya ce matsawar dai za a ce sai an je kotu ake iya tabbatar da wanda ya yi nasarar lashe zaɓe, to gaba ɗaya zaɓen duk ba shi da wani amfani.

“Saboda idan za a ci gaba da dogara da hukuncin kotu kafin a tabbatar da shugabanni a dimokraɗiyya, to zaɓen ba shi ma da amfani.

“Saboda ‘yan siyasar da ba su ci zaɓe ba za su iya zuwa kotu su yi ƙulle-ƙellen murɗe sakamakon zaɓe daga wanda ya yi nasara su kuma a ce su ne su ka yi.

“Babu yadda za a ce a kotu ne za a bayyana wanda ya ci zaɓen gwamna, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa da Majalisar Dokoki, to zaɓe ba shi da wani amfani.”

Gwamnonin da kotu ta naɗa a kotu na baya-bayan nan su ne Hope Uzodinma na Jihar Imo da Gwamna Duoye Diri na Bayelsa.

Dangane da matsalar yawan shari’un zaɓe, farkon makon nan ne INEC ta ce za ta ci gaba da bin umarnin kotu.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin umarnin da kowace kotu ta bayar a dukkan hukunce-hukuncen da su ka shafi zaɓe.

Shugaban hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, a lokacin da ya ke jawabi wurin buɗe Taron Alƙalai na Ƙara wa Juna Ilmi Kan Zaɓen, wanda aka yi ranar Litinin a Cibiyar Inganta Harkokin Shari’a (NJC), a Abuja.

“An shirya irin wannan zama kafin zaɓen 2019, inda aka yi bitar rikice-rikicen ƙararrakin da za su taso bayan zaɓe. Kuma wancan taron da mu ka yi ya yi tasiri sosai a lokacin.

“Saboda an samu raguwar hukunce-hukuncen da kotuna ke bayarwa masu cin karo da juna. Kuma an samu raguwar yawan zaɓen da kotuna ke sokewa masu yawan gaske,” inji Yakubu.

Ya gode wa manyan alƙalai da Hukumar Kula da Shari’a ta Ƙasa dangane wannan taro mai muhimmanci, wanda ya ce babu shakka zai rage yawan ƙararrakin zaɓe a kotuna.

Dangane da muhimmancin taron, Yakubu ya buga misali da irin matsalolin da ake samu a kotuna dalilin yanke hukunci masu karo da juna da kotuna ke yi.

“An fa wata kotu ta yi fatali da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, ta umarci INEC ta bayar da satifiket ɗin nasarar zaɓen fidda gwani ga ɗan takarar da Kotun Ƙoli ta soke zaɓen sa. To kun ga wannan cikar ne sosai ga hukumar zaɓe.

“Irin wannan kuma shi ke haifar da cinkoson shari’un zaɓe a kotu. Kuma an maida hannun agogo baya, tunda an sake shari’ar kenan wataƙila ma har sai an kai ga komawa Kotun Ƙoli.

Haka kuma shugaban na INEC ya nuna damuwa dangane da yawaitar ƙararrakin da aka haɗa da aka haɗa da sunan INEC aka maka kotu har sama da 600, a zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban.

“Ko kwanan nan wata jam’iyya ta zo a rana ɗaya ta kawo mana sunayen sabbin ‘yan takara 70 da ta ke so a cire sunayen na farkon da aka aiko mana, a maye gurbin su da sabbin da su ka kai mana,” Yakubu ya bayyana cikin damuwa.


Source link

Related Articles

15 Comments

  1. 👉 $5,000 FREE EXCHANGE BONUSES BELOW 📈 👉 PlaseFuture FREE $3,000 BONUS + 0% Maker Fees 📈 + PROMOCODE FOR NEWS USERS OF THE EXCHANGE 👉 [M0345IHZFN] — 0.01 BTC 👉 site: https://buycrypto.in.net Our site is a secure platform that makes it easy to buy, sell, and store cryptocurrency like Bitcoin, Ethereum, and More. We are available in over 30 countries worldwide.

  2. I would like to thnkx for the efforts you have put in writing this web site.
    I am hoping the same high-grade blog post from you in the upcoming as well.
    Actually your creative writing skills has encouraged me to get my own site now.
    Actually the blogging is spreading its wings quickly. Your write up is a good example of it.

    My blog post maid services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button