Labarai

2023: Zan tabbatar an yi sahihin zaɓe a Najeriya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da duniya cewa zai tabbatar da an shirya sahihin zaɓe a shekarar 23 kuma a cikin lumana.

Ya ce zai miƙa mulki salum-alum a cikin kwanciyar hankali bayan zaɓen 2023.

Buhari ya yi wannan ne a Taron Makama da Makomar Dimokraɗiyya, wanda Shugaban Amurka Joe Biden ya shirya, amma kowa ya halarta daga gida (virtaul).

Buhari ya ce za a ƙarfafa dukkan ɓangarorin da su ka dace domin tabbatar da Najeriya ta sake wanzuwa cikin miƙa mulki a cikin ruwan sanyi.

“Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ta marmatsawa, wanda za a yi cikin 2023, za mu inganta duk wasu hanyoyin da zaɓen zai zama sahihi, karɓaɓɓe kuma za a miƙa mulki a cikin ruwan sanyi.”

Buhari ya ce ya na maraba da haɗin kan manyan ƙasashen duniya wajen Inganta ɗorewar dimokraɗiyya a Najeriya, Afrika ta Yamma da ma Afrika baki daya.

Sai dai kuma ya koka tare da nuna damuwa ganin yadda masu ƙwatar mulki da ƙarfin tsiya ke wa dimokraɗiyya barazana.

A wani taron kuma, Birtaniya da duniya sun zuba-ido su ka yadda zaɓen Najeriya zai kasance ko ya kakare.

Jakadar Birtaniya a Najeriya Catriona Lang, ta bayyana cewa Afrika, Birtaniya da duniya baki ɗaya sun zuba ido domin ganin yadda zaɓen 2023 zai kasance ko ya kakare a Najeriya.

Lang ta yi wannan furuci a taron zaburar da matasa fiye da 200 na yankin Kudu maso Yamma da su ka yanke shawarar shiga takarar muƙaman siyasa daban-daban a zaɓen 2023.

Kungiyar Yiaga da ‘Not Too Young to Contest’ ne su ka zaburar da matasan.

Lang ta ce an zuba-ido a ga shin za a gudanar da zaɓe sahihi? Za a bari a gudanar da zaɓe sahihi? Shin zaɓen zai zama karɓaɓɓe a zukatan waɗanda su ka jefa ƙuri’a ko kuwa?” Inji Lang.

Lang ta ce ya zama wajibi a Najeriya a bar matasa da mata masu yawa su tsaya takarar muƙaman siyasa, domin su ma a dama da su a dimokraɗiyya.

A wurin taron, Gwamnan Kwara ya ce gwamnoni ba su faɗa da Sanatoci a kan salon zaɓen-fidda-gwani.

Gwamna AbdulRazak na Jihar Kwara ya bayyana cewa babu wani gwamna ko gungun gwamnonin da ke rigima ko jayayya da sanatoci a kan salon zaɓen fidda gwanin jam’iyya.

Ya bayyana haka ne a wurin bayanin da ya yi wa taron matasa fiye da 200 waɗanda su ka nuna sha’awar fitowa takardar muƙaman siyasa daban-daban.

AbdulRazak ya ce babu ruwan sa da wani salon zaɓe, ko za na wakilai ko na ‘yar tinƙi, wanda doka ta ce shi za a yi, to ya na maraba da salon.

Matasan sama da 200 sun yanke shawarar shiga siyasa ne bayan da ƙungiyar Yiaga Africa da ‘Not Too Young To Contest’ su ka zaburar domin su shiga muƙaman siyasa a dama da su.

An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwanonin Najeriya da sanatoci a kan salo da tsarin zaɓen fidda gwanin da jam’iyyun siyasa za su riƙa yi, wanda aka yi wa kwaskwarima a cikin Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda a yanzu ke gaban teburin Shugaba Muhammadu Buhari, ana jira kawai ya sa masa hannu.

Yayin da gwamnoni ba su goyon bayan dokar da ta ce a soke yin zaɓe a ƙarƙashin wakilai, a koma ‘yar tinƙi, su kuma sanatoci sun nuna goyon bayan ‘yar tinƙen.

Zaɓen fidda gwani a ƙarƙashin wakilai shi ne wanda wakilan jam’iyya ke yi. Shi kuma ‘yar tinƙe shi ne wanda kowane ɗan jam’iyya mai ɗauke da katin rajista da jam’iyya ke da haƙƙin yin zaɓe.

Gwamnan Kwara ya ce wa matasan amma dai shi tsarin zaɓen daga wakilai ya kai shi tsayawa takara. Kuma ba ya tsoron ko ma wane irin salon zaɓe.

“Sai dai ku matasa a matsayin ku na farkon shiga siyasa, zaɓen fidda gwani a ƙarƙashin wakilai zai fi sauƙi wajen tsayawar ku takara.

Cikin wannan makon ne wannan jarida ta buga labarin cewa INEC ta aika wa Buhari wasiƙa amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.

Sai dai kuma INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.

A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwanaki 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka kenan.

Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.

A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.

Sai kuma batun suka sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.

Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 Ga Disamba.

Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bila Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai tun daga mazaɓu har zuwa sama su riƙa yin zaɓen fidda-gwani.


Source link

Related Articles

203 Comments

 1. 444112 965541I dont feel Ive read anything like this before. So great to uncover somebody with some original thoughts on this topic. thank for starting this up. This internet site is something that is necessary on the web, someone with a bit originality. Great job for bringing something new towards the internet! 175934

 2. Pingback: 2cylinder
 3. ivermectin storage [url=https://ivermectin.beauty/#]stromectol 3 mg tablets price [/url] what happens if you overdose on ivermectin what happens when you put too much ivermectin in a bunny

 4. Netflix Türkiye, kullanıcılara iki yeni ödeme seçeneği sunmaya hazırlanıyor.
  Bankalararası Kart Merkezi (BKM) ve iyzico ile yapılan iş birliği sonucunda mevcut üyeler, aylık ücretlerini TROY logolu kartlarıyla
  ya da iyzico ile ödeyebilecek. iyzico bugün 35.000’den fazla küresel ve yerel online şirkete güvenli ödeme.

 5. Hamilelikte Bitkisel İlaç Kullanımı Gebelikte en az bir
  kez bitkisel ürün kullanımının Amerika ve Avusturalya’da ortalama %7-45, Çin’de
  %30-50 olduğu belirtilmektedir (1,2). Mavi cohosh özellikle de ilk trimesterde düşük
  yapıcı ve teratojenik etkilerinden dolayı kullanılmamalıdır (44,47).

 6. Magnezyum Çeşitleri ve Kullanım Şekilleri.
  Magnezyum takviyesi alırken, magnezyum sitrat, glisinat, aspartat gibi
  daha emilebilir formları tercih etmeniz öneriyoruz.
  Magnezyum karbonat, sülfat, glukonat daha ucuz olmakla beraber çok daha az emilebilir magnezyum çeşitleridir.
  Magnezyum Oksit. Bu form güçlü bir müshil etkisine sahip.

 7. Please stand by, while we are checking your browser… While many old-fashioned bookmakers offer their users a very limited betting line, we try to provide as many options as possible. As an example, let’s take a look at lines for a CS:GO match: There is a lot of debate about CSGO real money betting and skin gambling. Some say that skin gambling is by far the best option while others disagree. We tried both and here’s our take on CSGO real money betting vs skin gambling. One of the best advantages of using a PaySafeCard is that you are never going to have to pay any fees or charges when you purchase those vouchers or when you redeem them in any CS GO betting site account! Another way to prevent getting this page in the future is to use Privacy Pass. You may need to download version 2.0 now from the Chrome Web Store. https://louisicrh319864.therainblog.com/13944786/best-mobile-gambling-apps To withdrawal, select the same orange Deposit button and select the Withdrawal option. Minimum withdrawal is 0.002 BTC, or altcoin equivalent. You will need to confirm your email address to complete a withdrawal. Withdrawals take several minutes. Please stand by, while we are checking your browser… What are the Disadvantages of Bitcoin Dice?The disadvantages of Bitcoin Dice are a little bit harder to quantify. Because it’s not an area that has been focused on as fully as other types of casino games it does mean that players have access to a smaller range. This means that online dice players might not have the choice available to them that they want when playing Bitcoin Dice. Bitcoin dice gambling games follow pretty much the same gameplay and rules as its traditional counterpart in brick and mortar casinos, with two major differences. First, Bitcoin dice is provably fair. Players with a knowledge of crypto can check for themselves to ensure that the game is completely from any tampering or unfair advantages. The odds you see are the odds you play.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news