Labarai

A daina Kashe ƴan Arewa: Ƴan Najeriya sun roki Yarabawa

Dubban ƴan Najeriya musamman waɗanda ba ƴan yankin Arewa ba sun yi kira ga musamman Yarabawa da su daina karkashe ƴan Arewa da ke zama a yankin su.

Masu yin sharhi a kafafen sada zumunta dake yanar gizo sun yi tir da abinda ya faru a kasuwar Shasa dake jihar Oyo inda rigima tsakanin wani bahaushe yayi sanadiyyar rayuka da dukiyoyin ƴan Arewa musamman Hausawa dake jihohin yakin.

Musu yin sharhi sun ce tsame ƴan yanki ɗaya a rika kashe su ana muzguna musu ba shi da amfani ganin cewa kasar nan fa an warwatsu ne ta ko-ina.

Yadda rikicin Shasa ya yi sanadiyar rayuka da dukiyoyin ƴan Arewa

An rasa rayukan mutane da yawa a arangamar da ta faru tsakanin Hausawa da Yarabawa, a kasuwar Shasha, da aka fi sani da Sasa, Ibadan, Jihar Oyo.

Rikicin dai ya samo asali ne daga wata gardama tsakanin wasu mata biyu, daga nan fada ya kaure tsakanin wani Bayarabe da Bahaushe, har Bahaushen ya luma wa Bayarabe wuka, ya mutu.

Wanda aka burma wa wuka ya mutu a asibiti, ranar Juma’a, bayan caka masa wukar a ranar Alhamis.

Mutuwar sa ta harzuka Yarabawa, wadanda su kuma su ka yi dandazon daukar fansar kisan da Hausawa su ka yi wa dan uwan su.

Cikin kankanen lokaci sai tarzoma ta goce tun daga cikin kasuwar Shasha, har wajen kasuwa a cikin unguwar Sasa din.

Bangarorin biyu na Yarabawa da Hausawa sun rika kai wa juna hari, da sara, da kisa. Kamar yadda ganau ya shaida wa Premium Times.

“Akalla na ga gawarwakin mutum shida da su ka hada da Huasawa da Yarabawa. An rika banka wa shaguna da kantina na cikin kasuwa.

“Ganin haka kasuwa ta fashe kowa ya tsere kada rikici ya ritsa da shi.” Haka wani mai suna Khalid mazaunin Akinyele ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wani da rikicin ya faru a gaban sa, amma ba ya so a ambaci sunan sa, ya bayyana wa wakilin mu cewa wannan rikici bai bar kowa ba, domin ya shafi kowa.

“An koma gidaje masu yawa, kuma an kona shagunan cikin kasuwa da dama, kuma an lalata dukiyoyin ‘yan kasuwa. Jama’a da dama sun gudu sun bar gidajen su. Wasu kuma an kona wan a su gidajen wuta.”

‘Na Ga Gawarwakin Hausawa Birjik’

Washegari ranar Asabar kuma matasan Yarabawa ‘yan iska su ka tare hanyoyi, su na binciken motoci.

Duk inda aka ga Bahaushe a cikin mota, sai a fito da shi a rika dukan sa. Wasu kuma a wurin aka rika kashe su.

“In dai kai Bahaushe ne, to kawai za a fizgo ka daga cikin mota a kashe ka kawai. Wai su sun yi haka ne domin ramuwar kisan wani Bayaraben da aka ce wani Bahaushe ya yi a cikin kasuwar Shasha.”

Haka wani wanda ya shaida wa wakilin mu ya bayyana cewa da idon sa ya ga gawarwakin Hausawa birjik a unguwar Moyiwa a ranar Asabar.

Sai dai kuma daga baya an tura sojoji su ka fatattaki masu kisan Hausawa.

Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya shaida cewa komai ya lafa, kuma an gargadi cewa ba za a bari wasu batagari su haddasa fitina ba.

Yayin da gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma ke kiran a zauna lafiya da juna, haka wasu sanarakunan yankin da kuma ‘yan Najeriya da dama.

Tuni dai aka kakaba dokar hana fita a yankunan da rikicin ya kaure.


Source link

Related Articles

100 Comments

  1. Spot on with this write-up, I actually assume this website needs far more consideration. I will in all probability be once more to learn rather more, thanks for that info.

  2. This is really interesting, You’re a very skilled blogger. I have joined your feed and look forward to seeking more of your fantastic post. Also, I have shared your website in my social networks!

  3. Nevertheless, it’s all carried out with tongues rooted solidly in cheeks, and everybody has got nothing but absolutely love for their friendly neighborhood scapegoat. In reality, he is not merely a pushover. He is simply that extraordinary breed of person solid enough to take all that good natured ribbing for what it really is.

  4. I’ve read several good stuff here. Definitely worth bookmarking for revisiting. I surprise how much effort you put to make such a magnificent informative site.

  5. What’s Happening i’m new to this, I stumbled upon this I’ve found It positively useful and it has aided me out loads. I hope to contribute & help other users like its aided me. Great job.

  6. Pingback: 3metamorphosis
  7. I encountered your site after doing a search for new contesting using Google, and decided to stick around and read more of your articles. Thanks for posting, I have your site bookmarked now.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news