Labarai

A KARON FARKO A TARIHI: Matan Jihar Abiya za su fara cin gadon iyaye da na mazajen su

A karon farko a tarihi, Gwamantin Jihar Abiya ta kafa dokar raba gadon da mahaifi, mahaifiya ko mijin aure ya mutu ya bari tare da mata.

Gwamnan Jihar Abiya Okezie Ikpeazu ne ya bayyana cewa ya sanya wa dokar hannu, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna, mai suna Onuebuchi Ememanka ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba.

A ranar 16 Ga Nuwamba ne dai Majalisar Dokokin Jihar Abiya ta amince da dokar, wadda tun farko ƙudiri ce wanda Kakakin Majalisar Abiya, Chinedu Orji ya gabatar, kuma aka amince ta zama doka.

Gwamna Ikpeazu ya ce lokaci ya yi da za a daina nuna bambanci tsakanin mace da namiji, kuma gwamnatin sa ba za ta maida mata a matsayin jinsin da ke ƙasa da maza ba.

Ikpeazu ya buƙaci a yi watsi da tsohuwar al’adar tauye wa mata haƙƙi, a riƙa ba su duk wani haƙƙin da ya wajaba a riƙa ba su.

Idan ba a manta ba, cikin 2020 ne Kotun Ƙolin Najeriya ta haramta hana mata cin gadon da iyayen su ko mazan su su ka mutu su ka bari.

Kotun Ƙoli ta bayyana cewa ƙabilun da ke hana mata cin gadon iyaye ko mazan su, sun take Doka Sashe na 42(1) (a) da (2) na Kundin Dokokin Najeriya na 1999.

Gwamna Ikpeazu ya kuma jinjina wa Kakakin Majalisar Abiya, dangane da kawo wannan ƙudiri da ya yi a majalisa, har aka amince da shi ya zama doka.

A Najeriya akwai ƙabilu da dama waɗanda ba su raba gado da mata.

Musulunci dai ya wajibta raba gado da mata fiye da shekaru 1,400 da su ka gabata.


Source link

Related Articles

11 Comments

  1. Thank you for sharing superb informations. Your website is so cool. I am impressed by the details that you have on this site. It reveals how nicely you perceive this subject. Bookmarked this web page, will come back for more articles. You, my friend, ROCK! I found just the info I already searched everywhere and just couldn’t come across. What an ideal web site.

  2. Have you ever considered about adding a little bit more than just your articles? I mean, what you say is valuable and everything. Nevertheless just imagine if you added some great visuals or videos to give your posts more, “pop”! Your content is excellent but with pics and videos, this site could certainly be one of the greatest in its field. Very good blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close