Nishadi

A rika jika geron yin Kullin Koko cikin ruwan da aka hada da daskararren madaran shanu – Likitoci

Sakamakon binciken da wasu likitoci suka yi kan koko ko kuma kamu da ake sha sun gano cewa kullin kokon da aka hada shi da daskararren madaran shanu ya jiku kafin a nika ya fi inganci da kara karfin garkuwan jikin mutum fiye da wanda aka nika shi da ruwa zalla.

J. O. Omole, O. M. Ighodaro, and O. Durosinolorun dake koyarwa a jami’ar ‘ Lead City’ Ibadan, jihar Oyo ne suka gudanar da wannan bincike.

Sakamakon binciken ya nuna cewa man shanu na dauke da sinadarin inganta lafiya wanda idan aka hada shi a cikin kullun kokon da yara zasu sha zai inganta lafiyar su.

Likitocin sun ce za a iya amfani da sakamakon binciken da suka gano wajen inganta abincin da ake ciyar da yara musamman ga iyaye da kuma a makarantu.

Yadda za a hada daskararren madaran shanu cikin kullun kokon kuma ya ba da ma’ana

Idan aka dauko masara ko dawa ko gero ko Kuma a hada dawa da gero aka wanke sai a jika cikin wannan madara da aka narka na tsawon kwanaki uku.

Daga nan sai a kwashe hatsin sai a Kai nika.

Bayan an tace sannan kullin ya kwanta sai a kwashe a adana. Idan bukatar sha koko ko kamu ya tashi sai kawai a debo kullin ya dama.

Amfaninsa a jiki

1. Yana Kara karfin jiki.
2. Yana Kara karfin Ido.
3. Yana kara kaifin kwakwalwar yara.
4. Ya na dauke da sinadarin protein dake gina jiki.
5. Sannan ya na kara karfin garkuwan jiki.


Source link

Related Articles

62 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news