Ciwon Lafiya

A rungumi allurar rigakafin Korona hannu bibbiyu – Kiran Buhari ga ‘Yan Najeriya

Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suka yi allurar rigakafin korona a fadar shugaban kasa.

Likitan shugaban ƙasa Buhari, Sanusi Raafindadi da likitan Osinbajo, Nicholas Audifferen ne suka yi musu allurar rigakafin a gaban kwamitin PTF, wasu manyan jami’an gwamnati da manema labarai a fadan shugaban ƙasa.

Bayan haka ne Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su amince ayi musu allurar rigakafin cutar domin samun kariya daga cutar.

Buhari ya yi kira ga malaman addini, sarakunan da masu ruwa da tsaki da su ja ragamar wayar da kan mutane su amincewa da yin allurar rigakafin a kasar nan.

Kafin allurar rigakafin Korona ya dira Najeriya, mafi yawan wadanda aka tattauna da su don jin ra’ayoyin su sun ce ba su da ra’ayin yin rigakafin.

Babban abinda ya sa ba za su yi ba kuwa shine wai basu yarda da cutar ba, ballantana rigakafin cutar.

Sai dai kuma tun bayan da aka fara yi wa mutane harda shugaban kasa da mataimakin sa rigakafin cutar, sai aka fara tururuwan zuwa cibiyoyi da shafukan da ake rajistan yinrigakafin cutar.
Gamnati na bukatar ta tsananta yawar wa mutane kai game da alfanun yin rigakafin wanda hakan ya karanta matuka.


Source link

Related Articles

155 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button