Labarai

A wani mataki na kawo zaman zaman lafiya da haɗa kan juna tsakanin al’umma Fulani da sauran jama’a na jahar Adamawa

Arewa Youths Concern Media Forum

Duk al’ummar data tsinci kan cikin irin halin da al’ummar mu take a ayu na rashin hadin kai da kishin juna da rashin kokari wajen magance matsalolin da suka dabaibaye ta lalle akwai babban kalu bale a gaban ta. akwai bukatar al’ummar arewa mu hada kanmu waje guda ka rike akidar ka ta addini nima na rike tawa amma akwai maslahar rayuwa inda dole mu hadu koda addinin ya banbanta domin samarwa kan mu mafita balle addinin ya zama daya.

Yan Arewa bamuda hadin kai bama kishin junan mu bama kaunar juna. shi yasa yan ta’adda da azzaluman shuwagabanni sukeyin tasiri akan mu. shuwagabannin da suke mulkar mu suma sun yadda sun gaza matukar gazawa akan amanar da suka dauka domin Allah ya matse bakin wani jigo daga cikin shuwagabannin mu da sukayi sakaci da rayuwar mu a hannun yan ta’adda ya fada cewa lalle sun gaza akan shugabancin da sukeyi.

Amma fa duk da wannan ikirarin nasa dai fito neman wata takara bayan gama wa’adin sa na gwamna kuma wannan al’ummar da yace sun gaza wajen basu kariya su dasu kara zabar sa zuwa wani mukamin na dabam. in a wasu kasashe ne wannan ikirarin nasa kadai ya kai ya tilastashi yayi murabus tinda amfanin shugabanci shine abawa al’umma tsaro su samu aminci to shugaban da kansa yace ya gaza kuma yana ci gaba da gudanar da mulkin.

Babu wani wanda yake jin dadin abunda yake faruwa a Arewacin Nigeria tura takai bango baza kasan arewa tana fama da wasu manyan matsalolin ba sai ka zama wanda al’umma suke kawo kukansu gareka. wannan kungiya ta AYCMF kasancewar bama shiru akan al’amuran da suke faruwa a Arewacin Nigeria muna samun korafe korafe a sassa daban daban na yankin arewa akan irin matsanancin halin da al’umma suke ciki a hannun yan ta’adda sakamakon rashin kulawar shuwagabanni da daukar mataki akan yan ta’adda.

Wasu yankunan kamar Birnin Gwari na jahar kaduna da sabon Birni na jahar Sokoto da Isa duk a jahar Sokoto. da wasu yankunan jahar katsina kamar su shinkafi da yankunan zamfara. yadda gwamnati ta zuba ido ana cinmutuncin talakawa bayin Allah kai kace tamkar gwamnati kiwon yan ta’addan nan suke. kullum karfin su da izzar su da tozarcin da suke yi karu wa suke akan al’umma.

Shawara: zabe ne a gaban mu. muyi kokarin canja dukkan shugaban da ya gagara samawa al’ummar sa mafita a inda yake shugabanci. duk wanda ya gaza mazauna garin sun san ya gaza ba sai munce wane da wane ba.

Shawara: kar mu kuskure mu kara basu wata dama ta shugabancin mu. muyi kokarin zabo wasu mutanen koda a wata Jam’iya ce ba sai lalle APC da PDP. domin munada rashin wayewa a wajen zabe bama duba nagartar Mutum jam’iya muke dubawa jam’iyar ma manyan Jam’iyu muke dubawa wannan ba wayewa bane a siyasar dumukuradiya.

Shawara: duk abunda shuwagabannin nan da suka gaza dasu bamu na duniya mu karba amma mu kiyaye kara basu wata damar shugabancin mu domin baza su sauya ba. wanda ya gama gwamna shekara 8 kar mu zabesa sanata. wanda yayi shekara 4 a gwamna muyi kokarin hanashi tazarce. wanda yake sanata mu dawo dashi gida.

Tasirin Hadin Kai Ne Kawai Dai Bamu Damar Aiwatar Da Haka Wlh Wlh dukkan shuwagabannin nan in mukace damuyi sauyin su mu kawo wasu tare da kyakkyawar niya Allah dai dafa mana mukawo wanda dasu bawa rayuwar mu tsaro.

Amma in mukace ahaka damuci gaba da tafiya babu nazari babu lissafi baza muga da kyau ba Allah ya kiyaye.

✍️Sign AYCMF Management
2/4/2022


Source link

Related Articles

14 Comments

 1. Yesterday, while I was at work, my sister stole my iphone and
  tested to see if it can survive a 40 foot drop, just so
  she can be a youtube sensation. My apple ipad is
  now destroyed and she has 83 views. I know this is totally off topic but I had to
  share it with someone!

 2. Hello there, I do believe your blog might be having browser compatibility problems.
  Whenever I look at your website in Safari, it
  looks fine but when opening in IE, it has some overlapping issues.
  I just wanted to provide you with a quick heads up! Apart from that,
  wonderful website!

 3. Pretty nice post. I just stumbled upon your blog and wanted to say that I have really enjoyed
  browsing your blog posts. After all I’ll be subscribing to your feed and I hope you write again soon!

 4. Greetings! Quick question that’s entirely off topic.
  Do you know how to make your site mobile friendly?
  My website looks weird when viewing from my apple iphone.
  I’m trying to find a template or plugin that might be able to correct
  this issue. If you have any recommendations,
  please share. With thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news