Labarai

Abin da ya sa wasu ƴan Najeriya ke ɗaukar nauyin ta’addanci -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu a ƙasar nan na ɗaukar nauyin ta’addanci ne don su riƙe akalar tasirin su a cikin al’umma.

Da ya ke tattaunawa ta musamman da Gidan Talbijin na Najeriya, NTA a ranar Alhamis da Juma’a da dare, Buhari ya amsa tambaya dangane da mutanen da kwanan baya gwamnatin sa ta ce ta kama su na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a ƙasar nan, ya ce yawancin su hamshaƙan attajirai ne waɗanda ba su da sauran tasiri a cikin gwamnati.

Buhari ya ce waɗanda aka samu da laifi a cikin su za su fuskanci shari’a da hukunci a kotu.

“Wato hamshaƙai ne waɗanda ba su da sauran faɗa-a-ji, shi ne yanzu su ke amfani da dukiyoyin da su ka shafe shekara da shekaru su na tarawa wajen nuna cewa har yanzu su na da ƙarfin ƙwanji. Wannan gwamnatin za ta koya masu hankali.”

Sama da mutum 400 ne ‘yan leƙe asirin gwamnati su ka yi zargin su na ɗaukar nauyin Boko Haram.

Amma dai har yau a Najeriya ba a taba hukunta ko mutum ɗaya da aka ce an kama ya na ɗaukar nauyin Boko Haram a baya ba.

Idan ba a manta ba Gwamnatin Najeriya a kwanan nan kuma ta zargi Shugaban Tiwita da ɗaukar nauyin kuɗaɗen shirya zanga-zangar #EndSARS a kudancin ƙasar nan cikin watan Oktoba, 2020, zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa mummunar tarzoma.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa kamfanin Tiwita ya yi ladab, ya nemi zaman sulhuntawa da sasantawa da Gwamnatin Najeriya.

Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa halin da ake ciki tun bayan dakatar da Tiwita daga Najeriya.

Lai ya yi karin hasken ne bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Buhari a ranar Laraba.

Ministan ya kara jaddada cewa an karya fukafikin ‘yar tsuntsuwar Tiwita a Najeriya, saboda sun bayar da kofa ga wasu marasa kishin kasa su na amfani da kafar da nufin wargaza Najeriya.

Lai ya ce Shugaban Tiwita ne ya rika daukar nauyin dukkan kudaden da masu shirya tarzomar #EndSARS su ka kashe a lokacin zanga-zangar.

“Sannan kuma Tiwita ta bai wa Shugaban IPOB damar watsa sanarwar mambobin IPOB su rika kashe jami’an tsaro, kuma su rika banka wa kadarorin gwamnati wuta.”

Lai ya ce duk da Gwamnatin Najeriya ta yi ta rokon Tiwita cewa ta cire sanarwar Nnamdi Kanu da ya yi shelar a fara kisan ‘yan sanda ana banka wa kadarorin gwamnati wuta, Tiwita ta yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kirayen.

Daga ya lissafa sharuddan da ya ce tilas sai Tiwita ta cika kuma ta amince da su, kafin a amince ta ci gaba da aiki a Najeriya.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button