Wasanni

AFCON: Duk da kuranta ƴan kwallon Najeriya da Buhari yayi kai tsaye, sun ba ƴan kasa kunya, sun kwashi kashin su a hannu

Tun da ga fara wasa mai kallo ya san akwai alaman ƴan wasan Najeriya ba su zo su buga kwallon ƙafa yadda suka buga tsakanin su da ƙasar Egypt a farkon wasan cin kofin AFCON ba.

Abu kamar wasa duk da kuranta su da ake yi sai ga shi wankin hula ya kai Najeriya dare.

Lumuilumui kamar za a yi abin arziki ƴan Najeriya suka yi ta wasa za ayi kamar ba za ayi ba, haka dai har aka tafi hutun rabin lokaci.

Da aka dawo daga hutu sai ƴan Tunisia suka ce idan Najeriya ba ta yi ta ba su wuri, daga can nesa ɗan wasan Tunisia ya cilla kwallo ta ko zarce kai tsaye sai cikin ragar Najeriya.

Daga nan kuwa sai wasa ta canja zani, duk gayun da tsalle-tsalle da suke yi a filin sai ya tabbatar musu sai fa sai zage damtse.

Haka dai suka yi ta bugawa har dan wasa Alex Iwobi ya samu jan kati.

Wasa ya koma Najeriya na buga wasa da mutum 10 ne su kuma Tunisia da ƴan wasa 11.

Aje a dawo, a sheƙa can a dawo nan, abu dai kamar za ayi, ba za a yi ba har lokaci ya cika, alkalin wasa ya hura tashi.

Tunisia ta doke Najeriya da ci 1 – 0.


Source link

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news