Wasanni

Ahmed Musa zai koma West Brom

Ana kyautata zaton a cikin kwanakin nan masu zuwa fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya Ahmed Musa zai koma kasar Ingila da wasa.

Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito cewa lallai akwai yiwuwar dan kwallon zai koma kungiyar West Brom a cikin wannan wata ta Janairu kafina a rufe kasuwar siya da siyarwar ‘yan kwallo da aka bude tun daya ga wata.

Ahmed Musa dai yanzu ba ya buga kwallo a kowacce kungiyar kwallo kafa tun bayan ficewarsa daga kungiyar Nasr dake kasar Saudi Arabiya a shekarar bara.

Yanzu yana cin gashin kansa ne, mai rabo ka dauka.

Idan hakan ta yiwu Ahmed Musa zai taya kungiyar fita daga matakin na kusa da karshe a teburin Premier League wanda idan ba haka ba kungiyar kacokan za ta koma rukunin kwallon kafa na Championship a Ingila.

Ahmed Musa ya buga kwallo a Kasar Rasha, CSK Moscow daga nan sai ya koma kasar Birtaniya inda ya buga kwallo a kungiyar Leicester sannan kuma ya koma Kasar Saudiya.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button