Labarai

ALHERI DANƘO NE: Tinubu ne ya shiga ya fita ya sa aka naɗa ni Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas – Okiro

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mike Okiro, ya bayyana cewa ya zama Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas ne albarkacin ƙamun-ƙafa da Bola Tinubu, wanda a lokacin shi ne Gwamnan Jihar Legas.

Okiro ya ce Tinubu ne da kan sa ya rubuta wasiƙa ta musamman ya nemi a naɗa Okiro Kwamishinan ‘Yan Sanda na Legas.

Okiro ya bayyana haka a wani taron Mashahuran Mutanen da Tinubu ya yi wa Alfarma masu goyon bayan Takarar Tinubu/Shettima 2023.

Okiro ya yi Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2003 kafin ya zama Sufeto Janar na Ƙasa baki ɗaya a cikin 2007.

Shugaba Marigayi Umaru ‘Yar’Adua ne ya naɗa shi Sufeto Janar cikin 2007.

Okiro ya ce tsohon Sufeto Janar Musiliu Smith ne ya yi masa tiransifa zuwa Legas, bayan Tinubu ya rubuta masa buƙatar hakan.

Okiro ya ce ya san Tinubu tun zamanin gwagwarmayar NADECO, a lokacin ya na mataimakin kwamishinan ‘yan sanda a Legas ɗin, mai lura da fannin sintiri da kamen masu laifi.

Ya ce Tinubu ya buƙaci ya koma Legas saboda a lokacin ‘yan OPC da sauran maɓarnatan ɓatagari sun addabi Legas.

“Idan ka na so Legas ta yi tsaf a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, to ka maido Okiro a Legas.” Okiro ya ce haka Tinubu ya rubuta wa Musiliu Smith a lokacin.

“Ni Asiwaju Tinubu cikakken aboki na ne na haƙiƙa. Na san shi tun ina Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da Ikeja, lokacin gwagwarmayar NADECO. Ya gudu zuwa ƙasashen waje, ya dawo ya zama gwamna.”

Ya ce kuma Tinubu ne ya sa aka ƙara masa girma daga Kwamishinan ‘Yan Sanda zuwa Muƙaddashin Kwamishinan ‘Yan Sanda.

“Saboda ni fa babu wanda zann yi wa godiya sai Aiwaju Tinubu. Ba ni ko tantama cewa idan ya zama shugaban ƙasa, zai yi wa Najeriya irin gyaran da ya yi wa jihar Legas.”

Sauran waɗanda su ka yi jawabi a wurin sun haɗa da Umar Yakasai, wanda ya ce an zaɓi Okiro ya zama Shugaban Kwamitin Amintattun ne saboda kusancin sa sosai da Tinubu.

A ranar 28 Ga Satumba ne dai za a fara kamfen ɗin zaɓen 2023 gadan-gadan.


Source link

Related Articles

7 Comments

 1. I’ve been looking for photos and articles on this topic over the past few days due to a school assignment, safetoto and I’m really happy to find a post with the material I was looking for! I bookmark and will come often! Thanks 😀

 2. You actually make it seem really easy together with your presentation however I
  in finding this matter to be actually one thing which I feel I’d never
  understand. It kind of feels too complicated and very large for me.
  I am taking a look ahead in your subsequent submit, I’ll
  try to get the cling of it!

 3. You really make it seem so easy with your presentation but I find this matter
  to be actually something which I think I would
  never understand. It seems too complex and extremely broad for me.
  I’m looking forward for your next post, I will try to get
  the hang of it!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news