KannyWood

Ali Nuhu ya maka jaruma Hannatu Bashir a kotu bisa zargin cin zarafi

advertisement

JARUMIN Kannywood Ali Nuhu ya kai ƙarar babbar furodusa Hannatu Bashir a kotu bisa zargin ta ci masa mutunci ta hanyar gaya masa magana a saƙon tes.

Lauyar Ali, wato Salima Muhammad Sabo ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim & Co., ta shigar da ƙarar ne a Kotun Majistare mai lamba 58 da ke unguwar Nomansland a Kano.

Mujallar Fim ta gano cewa Ali Nuhu ya yi ƙarar ne saboda akasin da aka samu kan aikin wani fim na Hannatu wanda aka yi alƙawari da shi zai yi, amma ya saɓa.

A ranar da aka yi alƙawari da shi zai je ɗaukar fim ɗin, wato 10 ga wannan watan na Oktoba, an tafi aikin ɗaukar fim ɗin, amma sai Alin bai samu zuwa lokeshin ɗin ba domin ya yi tafiya, ba ya gari.

Rashin zuwan nasa ya sa tilas aka ɗage ɗaukar ɓangaren sa a aikin zuwa rana ta gaba, amma a wannan ranar ma bai je ba. Kamar yadda ya faɗa masu, ya ce sai a ranar ne ma zai dawo kuma ko ya dawo ma ba zai samu zuwa ba sai dai a rana ta gaba.

Wannan abin ya ɓata ran Hannatu Bashir, wadda ita ma sananniyar jaruma ce, don haka ta tura masa saƙo a waya ta ce masa ba ta ma buƙatar aikin da shi.

Saƙon, wanda mujallar Fim ta gani, ya sa shi ma jarumin ya mayar mata da martani mai zafi, ya ce ta yi masa rashin kunya. Daga ƙarshe ya faɗa mata zai ɗauki mataki na shari’a a kan ta. Ita kuma ta ce to ta na jiran shi.

A takardar ƙarar mai shafi biyu, wadda lauyar sa ta shigar, Ali ya shaida wa kotun cewa Hannatu, mai kamfanin Hanan Synergy Concept Limited, ta tura masa tes ne a ranar 10 ga Oktoba inda ta faɗa masa cewa ya ƙi zuwa yi mata aikin fim kuma hakan da ya yi mata bai dace ba kuma zalunci ne.

Ya ce ko kaɗan shi bai rattaba wata yarjejeniya da Hannatu ba cewa zai yi mata fim, kuma shi bai da wata hulɗar kasuwanci da ita da har za ta tura masa tes ta gaya masa baƙar magana wadda ɓatanci ne a gare shi tare da zubar masa da ƙima a idon jama’a.

Ya ce saboda haka ne ya ke so kotu ta ɗauki matakin shari’a na ɓata suna a kan Hannatu Bashir.

Ya ɗauki hoton tes ɗin da ta tura masa ya maƙala a takardar ƙarar domin kotu ta gani.

A turance, ƙarar da ya shigar ita ce “criminal direct complaint”, wadda zargin babban laifi ne.

A sammacin ƙarar, mai kwanan wata 11 ga Oktoba, 2022, wanda mujallar Fim ta gani, kotun ta buƙaci Hannatu Bashir da ta halarci zaman kotun a ranar 18 ga Oktoba domin ta kare kan ta.

Ana tsammanin wannan dai shi ne karo na farko da Ali Nuhu ya kai ƙarar wata jaruma a kotu.


Source link

Related Articles

3 Comments

  1. I’m writing on this topic these days, casinocommunity, but I have stopped writing because there is no reference material. Then I accidentally found your article. I can refer to a variety of materials, so I think the work I was preparing will work! Thank you for your efforts.

  2. As I am looking at your writing, casino online I regret being unable to do outdoor activities due to Corona 19, and I miss my old daily life. If you also miss the daily life of those days, would you please visit my site once? My site is a site where I post about photos and daily life when I was free.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button