Labarai

Alkali ya biya wa wani matashi sadakin naira N100,000 ya auri masoyiyar sa Bilkisu a Kaduna

Alkalin kotun shari’a dake jihar Kaduna Salisu Abubakar-Tureta ya biya wa wani matashi mai suna Salilu Salele sadakin aure naira N100,000 ya auri masoyiyar sa Bilkisu Lawal.

Alkali Abubakar-Tureta ya bayyana wa Salele da ya je ya yi nazari akan tayin da ya yi masa sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 6 ga Satumba.

Dama mahaifiyar Bilikisu, Rayila Lawal ta kai karar Salele kotu inda take bukatan kotu ta tilasta Salele ya auri ‘yarta Bilkisu idan har ya tabbatar yana kaunar ta ko Kuma ya rabu da ita idan har ya San bai shirya aure ba.

“A wuri daya muke zama sannan kulum yana zuwa wajen Bilkisu ba tare da ya nemi izinin mu iyayenta ba.

“Na yi wa mahaifiyar Salele bayanin abin dake faruwa amma ta ce danta bai shirya aure ba.

“Bayan haka sai Salele ya daina zuwa wurin Bilikisu a gida amma sai yana kiranta ta wayan suna haduwa a wani wuri.

“Na kawo karansa ne saboda bana so ya lalata tarbiyar da na bai wa ‘yata.

Raliya ta ce a shirye take ta aura wa Salele Bilkisu idan har ya shirya aure.

Salele ya bayyana a kotun cewa yana kaunar Bilkisu sai dai bai shirya aure ba sai nan da shekaru biyu masu zuwa.

“Ni dalibin daya daga cikin jami’o’in kasar nan ne amma ba zan so na raba hankali na biyu ba saboda aure ba.

“Bani da kudin biyan sadakin auren ta sannan har yanzu Ina zama tare da iyaye na ne. Inji Salele.


Source link

Related Articles

2 Comments

 1. I am not positive where you’re getting your
  information, however great topic. I needs to spend some
  time studying much more or working out more. Thank you for magnificent information I used to be on the lookout for this information for my mission.

 2. Admiring the time and effort you put into your
  site and in depth information you present. It’s great to come across a
  blog every once in a while that isn’t the same unwanted
  rehashed information. Wonderful read! I’ve saved your site and
  I’m including your RSS feeds to my Google account.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news