Labarai

Allah yayi wa sarkin Lere Janar Abubakar Mohammed (RTD) rasuwa

Da safiyar Asabar ne Allah ya yi wa Sarkin Lere na 13, janar Abubakar Mohammed II rasuwa.

Sarki Abubakar ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi.

Hussaini Mohammed, da ya ke tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar Sarki Abubakar, ya kara da cewa marigayin ya rasu bayan fama da yayi da yar gajeruwar rashin lafiya.

” Tun da ya tashi ba ya jin dadi da safen yau sai aka dauko zuwa Kaduna, amma kuma ko da aka iso sai likita ya ce ya rasu.”

Sarki Abubakar ya gaji babban wan sa Sarki Umaru Mohammed, wanda ya rasu a shekarar 2011.

Ya rasu ya bar ya’ya hudu da mata biyu.

Kafin sarki Abubakar ya dare kujerar sarautar Lere, ya rike mukamai da dama a Najeriya da suka hada da, gwamnan sokoto a 1985, sannan ya yi shugaban KADCCIMA a Kaduna.

” Marigayi sarki Abubakar II ya goya ‘ya yan yan uwa da karfafa zumunta a tsakanin mutanen masarautar Lere kafin Allah ya yi masa rasuwa.” In ji Mal Hussaini Mohammed.

Allah ya ji kan sa, Amin.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button