Labarai

ALLURA ZAI HAƘO GARMA: Mamu na da alaka da kungiyoyin ƴan ta’adda na Najeriya da Duniya sannan yana ba su bayanan sirri – In ji SSS

Hukumar tsaro na Sirri ta kasa, SSS ta zargi Tukur Mamu da yi wa kungiyoyin ƴan ta’adda na Najeriya da duniya aiki a boye.

Hakan na ƙunshia cikin rantsuwar da hukumar ta yi a kotu na a bata kwanaki 60 ta cigaba da tsare Muma har zuwa ta kammala binciken da ta soma a kan sa, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta buga

Idan ba manta ba, hukumar SSS ta kama Mamu bayan jami’an Interpol sun cafke shi a hanyar sa ta zuwa kasar Saudiya, inda suka maido shi Najeriya.

Bisa ga rahoton SSS, ” Ko tafiyar da Mamu zai yi zuwa kasar Saudiya, zai tafi ganawa ne da wasu jigajigan ƴan ta’adda kamar yadda bayanai suka nuna, inji SSS.

Bayan haka hukumar ta sanar da abubuwan da ta samu a binciken da ta yi a gidajen Mamu.

” Baya ga kuɗaɗen kasashen waje da aka samu an ga katin cire kuɗi ATM na bankuna dabandaban 16, takardar cire kuɗi (Cheque) 7, Komfuta (Laptop) 6, babbar Waya (Tablet) 4, wayoyin hannu 24, da kuma takardar fice da shige wato (Passport). An samu rigunan sojojin kasa 8 sai kuma rigunan sojojin ruwa 16.

Binciken farko-farko da aka yi an gano cewa akwai hannun Mamu a ayyukan ta’addanci da suka auku a kasar nan, in ji SSS.

” Wanda ake tuhuma (Mamu) ya yi amfani da aikin sa na ɗan jarida wajen taimaka wa kungiyoyin ta’addanci na gida da waje.

” Sannan kuma wanda ake zargin (Mamu) ya kitsa kashe jami’an tsaro da dama a yankin Arewa ta tsakiya da Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sannan kuma ya bayar da bayanan sirri a lokutta da yawa ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda wadanda suka ta’azzara ayyukan ta’addanci a Najeriya.


Source link

Related Articles

6 Comments

  1. An impressive share! I have just forwarded this onto a coworker who was doing a little research on this.
    And he in fact ordered me breakfast due to the fact that I stumbled upon it for him…
    lol. So let me reword this…. Thanks for the meal!!
    But yeah, thanx for spending time to talk about this topic here on your web page.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news