Labarai

Almajirai da mabarata sun kwararo Abuja – Mahukunta

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta koka kan yadda Almajirai da mabarata ke kwararowa cikin birnin Abuja.

Shugaban sashen hukumar da ke kula da walwalar jama’a Sani Amar ya fadi haka ranar Talata a wajen taron babban kwas na 44, 2022 na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa dake Jos suka ziyarci Cibiyar a Bwari Abuja.

Ya ce Almajirai da mabarata na kwararowa ne saboda rashin tsaron da ake fama da shi a wasu jihohin dake Arewacin kasar nan.

Amar ya kuma ce dokar kare hakkin dan Adam na UN da ya hana tsare mutum fiye da kwanaki uku baya taimakawa kokarin kawar da Almajirai da mabarata a Abuja.

Ya ce a dalilin haka ya sa duk kokarin da hukumar ke yi baya haifar da mai ido.

Amar ya ce a da idan ma’aikatan hukumar suka fita sukan kama mabarata da Almajirai 20 zuwa 25 a rana.

Amma yanzu komai ya canja, a rana ma’aikatan hukumar na kama mabarata sama da 100 idan suka fito aiki.

“A yanzu mabarata da muke kamawa mutane ne da basu da nakasa a jikinsu domin suna tafe ne da matan su da ‘ya’yan su.

” Sannan da dama daga cikin wadanda muka kama na yawo da damin kudi a jikinsu, kuɗade masu yawan gaske dankare a cikin kayan su ko aljifan su.

Ya yi kira ga jihohin dake makwabtaka da Abuja da su kirkiro tsare-tsare da zai taimaka wajen hana almajiranci da bara.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kafa dokar hana bara a duk fadin kasar nan domin kare mutane daga fadawa hannun masu damfara da sunan bara.


Source link

Related Articles

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button