Labarai

Amaechi ya bi sahun Lawal wajen taya Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaɓe, Osinbajo shiru har yanzu

Tsohon gwamnnan jihar Ribas, Rotimi Amaech ya mika sakon taya murna ga jagoran APC tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu bisa nasrar da ya samu a zaɓen fidda gwani na APC da aka yi a farkon wannan makon.

Amaechi ya ce ” Ina taya ka murnar nasarar da ka samu a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa da aka kammala ranar Laraba. Ina tabbatar maka cewa zan baka goyon baya na don ganin APC ta yi nasara a zaɓen dake tafe

Sai dai kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya zo na uku a zaɓen bai aika da sakon taya murnar ga Tinubu.

Osinbajo da ake ganin yana daga cikin ƴan siyasan da Tinubu ya goya amma ya yi kememe ya ki yarda ya janye masa a zaɓen fodda gwani sannan har yanzu bai aika da sakon taya murna ba ga sanata Tinubu.

A karshe dai shine ya zo ma uku a zaɓen inda Amaechi ya zo na biyu Ahmed Lawan ya zo na hudu.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news