Labarai

Ambaliyar ruwa ya yanke karamar hukumar Gulani daga yankin jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyan cewa ambaliyar ruwa ta hana shiga da fice daga karamar hukumar Gulani zuwa sauran bangarorin jihar.

Gwamna Buni ya fadi haka ne a wata takarda da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Mamman Mohammed ya saka wa hannuranar Litinin.

Buni ya ce ambaliyar ruwan ya mamaye hanyar Gujiba zuwa Gulani dake da nisan kilomita 500 dake kusa da jihohin Borno da Gombe.

Ya ce ambaliyar ya lashe gidaje da dabbobin mutane da dama a karamar hukumar.

Buni ya ce ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da na kasa da su gudanar da bincike domin gano iya barnan da ambaliyar yayi tare da samar da tallafi wa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Shugaban karamar hukumar Gulani Ilu Dayyabu ya ce ambaliyar ta ci gidaje da shaguna sama da 100 a kauyukan Kukawa, Bularafa da Bulunkutu.

Dayyabu ya ce hanya daya dake shiga kauyen Bukci da aka yi wa kwalbati, ambaliyar ya rusa shi.

Ya ce ambaliyar ya shafi kauyuka 9 daga cikin 12 din dake karamar hukumar.

Wadannan kauyuka sun hada da Sabai, Jibulwa, Bara, Gagure, Kushmega, Garin Tuwo, Teteba, Ruhu da Gulani.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button