KannyWood

Aminu Ala ya zama Ɗanburam Sarkin Gobir

“Farin ciki ba shi misaltuwa a daidai da ruwa ya koma kwari,

Na san ‘yan’uwa na na jini za su fi kowa farin ciki da wannan karamci, musamman ire-iren waɗanda  ko tushen su na asali ba su taɓa leƙawa ba, sai ga shi a yau tsuntsun da yai gabar ya dawo gida cikin karamci da yakana.

Madalla da wannan baiwa ta hikima daga Allah mai maida ɗa ga mahaifiyar sa ta asali.

Alhamdu lillahi Rabbil Alamina!”

 

KALAMAN fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (ALA) kenan a shafin sa na Instagram bayan ya karɓi takardar shaidar sarautar Ɗanburan Sarkin Gobir daga masarautar Gobir da ke Sabon Birnin Gobir, Jihar Sokoto.

 

Sarkin Gobir, Alhaji Isah Muhammadu Bawa, shi ne ya tabbatar masa da ba shi sarautar a wata takarda da ya rattaba wa hannu.

 

Idan ba a manta ba, ba wannan ba ce sarautar da Ala ya fara samu; ya samu sarautu daga masarautun gargajiya na Arewa daban-daban. 

 

Takardar bai wa Ala sarautar Ɗanburam Sarkin Gobir ɗauke da hatimin sarkin

 

Ala ya fara samun sarautar Ɗan Amanar Bichi a lokacin da Alhaji Aminu Ado Bayero ya na Sarkin Bichi kafin ya zama Sarkin Kano. Sai kuma Sarkin Ƙaraye, Dakta Ibrahim Abubakar II, ya ba shi sarautar Dujuman Ƙaraye. 

 

Haka Sarkin Dutse a Jihar Jigawa, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, ya naɗa shi Sarkin Waƙar Dutse, wanda har bikin naɗin aka yi a garin Dutse a shekarar da ta gabata.

 

A yanzu dai mawaƙin sarautun sa huɗu kenan.

 

Shi dai Ala, da ma tsatson sa daga Gobir ne. Kamar yadda ya sha faɗa a tarihin sa, iyayen sa da kakannin sa ‘yan asalin Kebbi ne, zama ya kai su Kano inda aka haife shi. 

 

Mu na fatan Allah ya taya shi riƙo.

 

Fostar taya sabon Ɗanburam murna
Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button