Labarai

An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, ya ce aƙalla akwai tubabbun ‘yan Boko Haram cike fal da sansani uku da aka tanadar masu.

Zulum ya yi wannan ƙarin bayani a lokacin da ya ke ƙaddamar da kwamitin maido ‘yan Jihar Barno da ke hijira a ƙasashen Nijar, Chadi da Kamaru.

Da ya ke ƙaddamar da kwamitin, Zulum ya ce aikin kwamitin zai kasance dawo da masu gudun hijira da kuma kula da tubabbun ‘yan Boko Haram, musamman yadda za su riƙa fitowa daga cikin jeji, kyautata rayuwar su da kuma maida su cikin jama’a.

Zulum ya ce matsawar aka kula da aiwatar da tsarin da kyau, kwamitin zai samu nasarar samun yawaitar masu tuba su na ajiye makaman su.

Hakan kuwa a cewar sa, zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar baki ɗaya.

Zulum ya bayyana cewa ita ma Gwamnatin Tarayya ita ma ta kafa kwamitin dawo da waɗanda su ka yi hijira daga Najeriya zuwa cikin wasu ƙasashen da ke maƙautaka da Najeriya.

Yayin da kwamitin jihar Barno ke ƙarƙashin Mataimakin Gwamna Umar Kadafur, shi kuwa kwamitin da Gwamantin Tarayya ta naɗa ya na ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, kuma zai riƙa yin aiki tare da tuntuɓar kwamitin Jihar Barno.

Sai dai kuma Zulum ya nuna damuwar cewa a yanzu haka sansani ukun da aka ware don ajiye tubabbun ‘yan Boko Haram, ya cikal fal.

Ya ce gwamnatin jihar ta tattauna da Babban Kwamandan Sojojin Barno, domin a samu wasu manya-manyan sansanonin ajiyar tubabbun.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button