Labarai

An damke wanda ya taushe yarinya mai tallar kosai ta mutu garin yi mata fyade

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe sun damke wani mutum mai suna Sani Sale, mai shekaru 38 da ya tsere bayan wata karamar yarinyar da ya yi wa fyade ta mutu a dakin sa.

Sale ya yi wa yarinyar mai shekaru 15 fyade ne a dakin sa a jihar Yobe, amma sai ya gudu zuwa Jihar Gombe.

Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Gombe, Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa Sani Sale aikin makaneza ya ke yi a garin Gadaka, cikin Karamar Hukumar Fika, kuma a Gadaka din ne ya danne karamar yarinya ya rika lalata da ita, har ta mutu.

Ya kara da cewa yarinyar ta bar gida dauke da tallar kosai a ranar 10 Ga Fabrairu, amma da aka ga yamma ta yi, sai aka fara cigiyar ta, da aka ga ba ta koma gida ba.

Dungus ya kara da cewa bayan an tsananta bincike, sai aka gano yarinyar cikin dakin Sani Sale.

“Ranar 11 Ga Fabarairu, 2021 ne jami’an bincike daga Ofishin ’Yan Sandan Fika ta Jihar Yobe su ka damke Sani Sale mai shekaru 38, a Gombe.

“Sun zo sun kama shi bayan ya yi wa karamar yarinya mai shekaru 15 fyade har ta mutu a garin su, wato Gadaka.

“Bincike ya tabbatar da cewa an gano yarinyar a dakin sa, bayan ya gudu a ranar 10 Ga Fabrairu, 2021. Yarinyar kosai ta ke sayarwa, amma ya kai ta dakin sa ya yi mata fyade.”

Haka sanarwar ’yan sandan Gombe ta bayyana, ta bakin Dungus Abdulkarim

Ya ce yanzu Sani Sale ya na hannun ‘yan sandan Gombe, amma za su damka shi a hannun ‘yan sandan Fika, inda daga can kuma za a zarce da shi ofishin CID na Yobe domin ci gaba da bincike.

Ya ce jami’an yan sandan Gombe su ka taya jami’an Yobe damke Sani Sale a cikin Gombe.


Source link

Related Articles

85 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button