Labarai

An gano gawakin sojoji yashe a jeji bayan harin da yan bindiga suka kai sun kuma yi awongaba da shugaban su a sansanin

Hon. Barr Bala Silas Sanga dai tsohon Kwamishina ne a ma’aikatar harkokin shara’a na jahar Adamawa, Bala dai ya sayi Form na neman takaran kujerar Sanata da zai wakilci kudancin jahar Adamawa

Barr Bala dai masani ne kan harkokin Shari’a kuma ya bada gudummawar shi da dama akan harkokin Shari’a koda a shekara ta 2019 shine Kwamishina a ma’aikatar Shari’a na jahar Adamawa

Kuma Barr Bala ya jagoranci manya manyan shara’a a jahar Adamawa dama Nigeria baki ɗaya wannan ya baiwa Barr damar samun ƙorewa tare da tuna hanyoyin taimakawa al’umma

Bala dai zai shigo harkar siyasa ne kasan cewar irin gudummawar da yayi ta badawa a baya ko da ganin irin wasu damammaki da Bala ya samu a wasu lokuta da suka gabata, ya gina kotu a ƙananan hukumomi 2 dan sauwaƙawa mazauna wannan yankin zuwa wuraren shara’a

Hasilama dai yana ƙoƙarin gabatar da wasu ayyuka da dama yanzu haka da zasu taimaki rayuwar jama’a Bala nada kyakkyawar alaƙa da wasu ƙungiyoyin ƙasashen waje da zasu iya taimakawa al’ummar

Bala dai zai yi takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyar APC Mai mulki a Najeriya ya kuma kammala dukkan nin shirye-shiryen tsayawa takaran, ya kuma samu goyon bayan jama’a matuƙa fata dai Allah yabada Sa’a da Nasara


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news