Ciwon Lafiya

An hau hanyar sasantawa tsakanin NARD da Gwamnatin Tarayya

A ranar Laraba ce Mai Shari’a Bashir Aliyu na Kotun Sauraren Ƙararrakin Ƙwadago (National Industrial Court) ta Abuja, ya umarci ɓangarori biyu na Gwamnatin Tarayya da kuma Kungiyar Litikitocin NARD masu yajin aiki, cewa ya ba su nan da zuwa Juma’a su koma kan teburin tattaunawa tsakanin su.

Hakan ya biyo bayan ƙarar da ke gaban alƙalin, wadda dambarwa ce wadda ta samo asali tun daga ranar da likitocin NARD su ka fara yajin aiki, a ranar 2 Ga Agusta, 2021.

Yayin da likitocin su ka ce ba za su koma aiki ba, sai Gwamnantin Tarayya ta biya su haƙƙoƙin su, ita kuma Gwamnantin Tarayya ta bakin Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, ta ce ba za ta sake biyan su albashi ba, sai sun koma aiki.

A kotun dai an yi doguwar musayar maganganu tsakanin lauyan gwamnati, babban lauya Tobichukwu da kuma lauyan Ƙungiyar Likitocin NARD, Femi Falana.

Daga ƙarshe dai Mai Shari’a ya ce a koma teburin sulhu, kuma duk yadda sakamakon sulhu ya kama, to a kawo masa a rubuce a ranar Juma’a, domin ɗorawa daga inda aka tsaya.

Cikin watan Agusta Minista Ngige ya fusata ya bayyana cewa likitanci a Najeriya ya shiga garari da gararamba.

Ya yi bayanin ne ganin yadda ya kasa shawo kan likitocin domin su janye yajin aikin da su ke yi.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya yi gargaɗin cewa aikin likita a Najeriya ya shiga garari da gararamba, ganin yadda likitocin ƙasar nan su ka maida yajin aiki kamar wani abin tinƙaho a rayuwar su.

Ngige ya yi kira ga likitoci su daina ɗagawa da girman kai, saboda su na ganin kamar su ne ke ceton rayukan mutane.

Minista Ngige na magana ne a kan yajin aikin da Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa (NARD) ke yi tun a ranar 2 Ga Agusta.

Ya yi wannan bayani ne a Taron Ƙungiyar Dattawan Likitoci, wanda aka yi a Abuja.

A taron an tattauna Matsayin Aikin Likita a Jiya da Yau da kuma Gobe.

“Ba a taɓa samun lokacin da aikin likitanci ya shiga mummunan hatsari a ƙasar nan kamar a halin da mu ke ciki a yanzu ba. Daga inda na ke tsaye a nan ko zaune, ina hango gagarimar matsala a wannan fanni ta tunkaro ƙasar nan.

“Likitoci ba su tashi yajin aiki sai lokacin da likita ɗan uwan su ke kan muƙami. Minista Onyebuchi Chukwu da Minista Adebowale duk sun sha fama da yajin aiki a baya.

“Ga shi daga hawa na tsawon shekaru shida kenan, amma an yi min yajin aiki sau huɗu. Wasun mu kuma duk mun yi waɗannan ƙungiyoyi, musamman NARD.”

Da ya ke magana, Shugaban Ƙungiyar Likitoci Gaba Ɗaya ta Najeriya (NMA), Innocent Ujah, ya bayyana halin ƙuncin da likitocin Najeriya ke ciki, kuma su ke ci gaba da fuskanta daga manyan su har ƙanana.

Ya koka dangane da yadda Hukumar Tsara Albashin Ma’aikata (NSIWC) ta fitar da sanarwar za a daina biyan likitocin da ke koyarwa a jami’a alawus ɗin CONMESS.

Sannan ya yi ƙorafin yadda duk ilimin ka in dai kai likitanci ka ke koyarwa, to ba za a zaɓe ka shugabancin Jami’ar Jihar Legas ba.

Ujah ya ce haka kawai ana jin haushi da ganin ƙyashin likitoci, ba tare da yin la’akari da irin shekarun da su ke shafewa wajen neman ilimi ba, da kuma irin hatsarin da su ke shiga wajen gudanar da aikin su.

Ƙungiyar Likitocin NARD ta tsunduma yajin aiki, saboda gwamnati ta ƙi cika masu alƙawarran biyan su haƙƙoƙin su da ta ɗauka a rubuce tsawon watanni fiye da uku da su ka gabata.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button