Ciwon Lafiya

An samu karin mutum shida da suka kamu da cutar, mutum daya ya mutu a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa an samu karuwar wasu mutum shida da suka kamu da cutar zazzabin lassa a Najeriya.

Hukumar ta ce ta kuma yi ajalin mutum daya a kasar nan.

An gano wadannan mutane a jihohin Ondo da Bauchi daga ranar 19 zuwa 25 ga Satumba.

Zuwa yanzu mutum 929 sun kamu, kuma cutar ta yi ajalin mutum 172 a kananan hukumomi 103 dake jihohin 25 a kasar nan.

Duk da adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a shekaran 2022 ya kai kashi 18.5% sannan a shekaran 2021 mutum kashi 23.0% be suka kamu da cutar.

Jihohin Ondo, Edo da Bauchi na daga cikin jihohin da cutar ta fi yi wa katutu a kasar nan.

Har yanzu dai babu jami’in lafiyan da ya kamu ko ya mutu daga cutar.

Zazzabin Lassa

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

ALAMUN KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA

Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.

Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.

Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.

Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.

Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.

Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.

Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.

Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.

Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da Zazzabin Lassa

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.


Source link

Related Articles

3 Comments

  1. Nice blog! Is your theme custom made or did you download it from somewhere? A theme like yours with a few simple tweeks would really make my blog stand out. Please let me know where you got your design. Thanks

  2. I like the helpful info you provide in your articles. I’ll bookmark your blog and check again here frequently. I am quite sure I’ll learn plenty of new stuff right here! Best of luck for the next!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button