Labarai

An yanke wa sojan da ya kashe soja hukuncin kisa ta hanyar bindigewa

Kotun Cikin Gida ta Sojoji ta yanke hukunci kisa ta hanyar bindigewa kan wani soja mai suna Azunna Mmaduabuchi.

An samu Mmaduabuchi ne da laifin bindige wani soja da ke sama da shi a mukami.

An ruwaito yadda sojan ya bindige Laftanar Babankaka Ngorki a cikin watan Yuli, 2020, inda nan take ya mutu.

A sanarwar yanke hukuncin dai ba a bayyana ko akwai wata jikakka tsakanin sojan da ya yi kisan da kuma wanda ya kashe ba.

Sojan da ya yi kisan dai ya amince cewa ya yi kisan tabbas, amma ya ce tsautsayi ne, ba da gangan ba.

Sai dai kuma PREEMIUM TIMES ta tabbatar daga wata majiya cewa sojan da aka yanke wa hukuncin kisan ya taba yin tafiyar sa ya bar aikin soja, tsawon watanni shida.

Wannan ya sa aka tsaida albashin sa tsawon watanni shidan da ya yi ba a san inda ya ke ba.

PREMIUM TIMES ta ji cewa bayan sojan ya dawo aiki an hana shi allbashin sa na tsawon watanni shidan da ya yi ba ya wurin aiki, sai ya roki na sama da shi din, wato wanda ya ke a karkashin sa, Laftanar Ngorgi kenan da ya ba shi izni ya tafi babban birnin jiha ya warware matsalar albashin sa da aka dakatar. Shi kuma Ngorgi ya hana shi tafiya, ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba.

To ba a sani ba ko wannan ne dalilin da ya sa sojan ya fusata a karshe har ya dirka wa Ngorgi bindiga ba.

Shaidar Wadanda Aka Yi Kisa A Gaban Su:

Masu bada shaida su takwas sun shaida wa kotun wadda Arikpo Ekubi ya shugabanta cewa sun ga sojan da ya yi kisan tsaye da bindiga kirar AK47 ya na rike a daidai inda shi kuma Ngorgi ke kwance a cikin jini male-male.

Wani kuma cikin masu bada shaidar ya shaida wa kotun cewa wanda ya yi harbin ya same shi ya na tafiya, amma ya wuce shi, ko gaida shi bai yi ba, a matsayin sa na wanda ke gaba da shi.

“Haka ya wuce ni ko magana bai yi mani ba. Ya je ya samu Ngorgi ya na waya, kawai ya dirka masa bindiga.

“Bayan ya kashe shi, sai kuma ya juyo kai na, ya bube ni sannan ya daga hannuwa sama, ya ce min “shikenan, na kashe shi!”

Kotu dai ta ce sojan da ya yi kisan ya kasa bada hujjar cewa tsautsayi ne.

“Wanda ya yi kisan ya yi baki-biyu. Na farko a rubutaccen bayanin yadda kisan ya faru, ya ce bindigar sa ce ta tashi a daidai lokacin da ya je wucewa ta kusa da wanda ya kashe din.

“Amma kuma a jawabin da ya yi wa kotu a lokacin da aka ce ya tashi ya nuna yadda ya ke rike da bindiga a lokacin, sai ya ce ai bindigar ta tashi a lokacin da ya ke dibar ruwa.”

A karshe dai kotu ta gamsu cewa da gangan ya kashe Ngorgi, soja mai mukamin Laftanar, mai lamba N/16439 aiki a matsayin Adjutant, a Bataliya ta 202.

Sannan kuma kotun ta daure wasu sojoji hudu kan wa’adin shekaru daban-daban a hannun da su ke da shi wajen musabbabin rasa ran wani farar hula, ta hanyar gallaza masa azaba.

An kuma daure wani soja mai suna Muhammed Kuru shekara uku, saboda aifin dirka bindiga da ya yi a wurin taron biki, har ya yi sanadiyyar mutuwar wani yaro dan shekara 11.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button