Labarai

An yi amfani da ƴan daba ne aka kada ni – Bashir Ahmed

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kafafen ƴaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmed ya sha kasa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda aka yi a Kano ranar Juma’a.

Bisa ga sakamakon zaben da aka bayyana bayan da wakilai suka kaɗa kuri’a Bashir ya samu kuri’u 11 ne kacal, inda Mahmud Gaya, wanda yake kan wannan kujera, ya samu ƙuri’u 109.

Ahmed ya rubuta a shafin sa ta Facebook cewa ” Ba zan iya cigaba da zama a wannan wuri na zaɓe ba saboda amfani da ƴan daba da ake yi wajen muzguna wa wakilai.

Daga nan sai ya ta shi ya fita abinsa yana ta babatu da zargin murdiya da ka yi masa kamar yadda ya bayyana.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button