KannyWood

An yi taron duniya kan finafinan Afrika ba tare da ‘yan Kannywood ba

AN kwashe tsawon kwana biyu ana gudanar da taron duniya kan finafinan harsunan Afrika na gado, amma masu shirya finanan Hausa ba su halarta ba.

A yau ne aka kammala taron a Kano.

A taron, Shugaban Tsangayar Aikin Jarida ta Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Mustapha Nasiru Malam, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a samar da ƙananan kwasa-kwasai a jami’ar domin ƙara wa masu sana’ar shirya fim ilimi.

 

Malamin ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar bayan  kammala taron yini biyu kan yadda ake gudanar da bincike da rubuta labaran finafinai cikin harsunan Afrika, wanda aka yi a yau a Kano.

 

Taron, wanda aka fi sani da ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), an gudanar da shi ne ta hanyar tsarin ga-ni-ga-ka ta manhajar Zoom.

 

Ɗimbin jama’a sun mahalarci taron ta hanyar Zoom

 

Kuma an yi shi ne tare da haɗin gwiwa tsakanin kamfanin shirya finafinai na Moving Image da ke Kano da Tsangayar Aikin Jarida ta Jami’ar Bayero, Kano (BUK).

 

Farfesan ya ƙara da cewa haɗin kan nasu ba zai tsaya iya shirya wannan taron ba, domin kuwa tsangayar za ta ci gaba da haɗa kai da kamfanin Moving Image, mai shirya taron na shekara-shekara, don ganin an ciyar da harkar shirya finafinai gaba. 

 

A nasa jawabin, shugaban Moving Image kuma jagoran shirya taron, Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana farin cikin sa ganin yadda su ka gabatar da taron a karo na uku cikin kwanciyar hankali tare da samun haɗin kan al’umma, musamman waɗanda su ka halarta.

 

Bugu da ƙari, ya yaba wa Tsangayar  Aikin Jarida ta BUK kan irin gudunmawar da ta bayar wajen ganin an yi taron lafiya ba tare da tangarɗar kayan aiki ba.

 

Wasu mahalarta taron

 

A yayin taron, an gabatar da maƙaloli kimanin 22 waɗanda su ka fito daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasar waje.

 

Masu gabatar da maƙalolin sun fito daga Kano, Legas, Abuja, Jamus da sauran su daga jami’o’i, kwalejojin fasaha da na iliimin aikin koyarwa.

 

Sai dai har zuwa lokacin kammala taron, mujallar Fim ba ta ga ‘yan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood a ciki ba duk da irin kiraye-kirayen da aka yi kan su fito su rungumi wannan tsarin domin taimaka wa cigaban sana’ar tasu.

 

Lokacin gudanar da taron

 

Idan kun tuna, mujallar Fim ta kawo maku tattaunawar da ta yi da Alhaji Abdulkareem Muhammad a game da taron, inda ya bayyana irin ƙalubalen da su ke fuskanta kan shirya taron, musamman ƙin shiga taron da ‘yan Kannywood su ka yi.
Source link

Related Articles

159 Comments

  1. You are so interesting! I don’t suppose I’ve truly read something like that before. So wonderful to find somebody with genuine thoughts on this topic. Seriously.. thank you for starting this up. This website is something that’s needed on the web, someone with a bit of originality!|

  2. Hey There. I found your blog using msn. This is a very well written article. I’ll make sure to bookmark it and come back to read more of your useful information. Thanks for the post. I’ll certainly return.|

  3. Greetings! Quick question that’s completely off topic. Do you know how to make your site mobile friendly? My website looks weird when browsing from my apple iphone. I’m trying to find a theme or plugin that might be able to resolve this problem. If you have any suggestions, please share. Cheers!|

  4. I am really impressed with your writing skills and also with the layout on your weblog. Is this a paid theme or did you customize it yourself? Either way keep up the nice quality writing, it is rare to see a great blog like this one these days.|

  5. Good post. I learn something totally new and challenging on sites I stumbleupon everyday. It’s always interesting to read through articles from other writers and practice something from their web sites. |

  6. wonderful submit, very informative. I wonder why the other specialists of this sector don’t notice this. You must proceed your writing. I am confident, you have a great readers’ base already!|

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button