Labarai

An zargi wasu ƴan bindiga da farwa matasa a dajin Dong na ƙaramar hukumar Numan a jahar Adamawa.

An kaddamar da dalar buhunan masara a jihar Kaduna, a wani yunƙuri da hukumomi ke cewa na nuna irin ci gaban da aka samu a ƙasar ta fuskar noman masarar.

Shirin dalar masara tsari ne na hadin-gwiwa tsakanin ƙungiyar manoman masara da Babban bankin Najeriya wato CBN, karkashin shirin bada tallafi ga manoma na Anchor Borrower Programme.

Ana saran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar wadanda suka samu tallafin Anchor Borrower Programme.

Wannan na zuwa ne sama da mako biyu bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar, in ji gwamnatinsa.

Shugaban kungiyar manoman masara ta Najeriya, Alhaji Bello Abubakar Funtuwa ya shaidawa BBC cewa an tara dalar masara ce don bayyana wa duniya irin nasarorin da aka samu a noman masara a ƙasar.

Ya ce rancen da ake bai wa manoma ya taka rawa wajen bai wa manoma damar tara irin wannan masara, kuma wannan somin-taɓi ne.

“Duk da cewa suna fuskantar matsalolin tsaro a kauyuka, hakan bai hanasu tara masara ba. Amma muna fatan tsaro ya inganta, saboda noman ya fi wanda aka gani a yanzu.”

Shirin na gwamnatin na zuwa ne adaidai lokacin da ‘yan kasa ke kokawa da yadda kayan abinci ke tashin gauron-zabi, inda a yanzu haka buhun masarar na kai wa dubu 22.

Wannan dalilin ne ya sanya BBC ji daga bakin mahukunta kan ko kaddamar da wannan dala za ta sauya farashi ko akwai wani sauyi da za a gani.

Mal Ibrahim Husseini, shi ne kwamishinan Noma da ya wakilci gwamnan Kaduna a wajen kaddamar da dalar masarar, wanda ya shaida mana cewa kasuwa ce ke tabbatar da farashi.

Kwamishinan ya ce abu muhimmin a yanzu shi ne kokarin tabbatar da wadatuwar abinci a kasar.

“Wannan tsari tabbas farashi ya sauka da lokaci, kuma manoma ke sayar da kayansu ba za a kayyade musu ba, ya danganta amma suna kan tsrai.”

Ana saran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar

Karin haske

Gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa tana daukan matakan bunkasa harkar noma domin rage abinci da ake shigar da su kasar daga ketare

Shugaba Buhari a lokacin kaddamar da irin wannan dala amma ta shinkafa a watan Janairu ya ce ana samun irin wannan nasara ne sakamako juye-juyen halin da gwamnatinsa ta ƙaddamar ta fuskar noma domin tabbatar da cewa ƴan Najeriya na iya noma abin da za su ci kuma su ci abin suka noma.

Gwamnati dai ta ce kawo yanzu shirin Anchor Borrowers ya tallafa wa ƙananan manoma miliyan 4.8; wajen noma nau’ukan amfanin gona har iri 23 da suka haɗa da shinkafa, da masara da kwakwar manja, da koko, da auduga, da rogo da tumatur da kuma wajen kiwon dabbobi.


Source link

Related Articles

9 Comments

 1. Excellent post. I was checking constantly this blog and I am impressed!
  Very useful information specifically the last part 🙂 I care for such info much.
  I was looking for this certain info for a very long time. Thank you and best
  of luck.

 2. Hi, i read your blog occasionally and i own a similar one and
  i was just wondering if you get a lot of spam feedback?
  If so how do you prevent it, any plugin or anything you can suggest?

  I get so much lately it’s driving me crazy so any assistance is
  very much appreciated.

 3. A personalized a lot of an excellent relations and peeks really
  talented video musician. Really should you are sickness also obstacle our own site traditional.

  Following obtaining focused on world wide web traffic might especially forlorn in addition to elegance.
  Thinker, we devote time and energy to recover our personal lifestyle is around ones difficulty with
  a better?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news