Labarai

Ana batakashi tsakanin ‘yan ta’adda da Sojojin Najeriya a Madallah Abuja

Rahotanni da suka iske mu a wannan lokaci sun nuna cewa sojojin Najeriya na batakashi da ‘yan Ta’adda a Madalla, dake kusa da Abuja.
Masu motoci sun fice daga motocin su kowa ya arce sanadiyyar wannan arangama da sojoji ke yi da ‘yan ta’adda.

Yan ta’adda sun far wa sojoji a shingen da aka kafa domin binciken motoci a Madalla dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja.

Wannan harin ya biyo bayan wanda ‘yan bindiga suka kai wa tawagar sojojin da ke gadin shugaban kasa a Bwari.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button