Ciwon Lafiya

ANA WATA GA WATA: Sabuwar nau’in Korona da ta bulla a Birtaniyya ta bayyana a Najeriya

A watan Satumba Kasar Birtaniya ta sanar da bayyanar wata sabuwar samfurin Korona da take mamaye mutanen kasar sannan ana samun karin mutanen kasar da ke ta mutuwa babu kakkautawa.

Masana kuma likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID, na jami’ar Redeemers dake jihar Osun.

Ita dai wannan nau’i na Korona mai suna “lineage B.1.1.7” ta bayyana da zafi a kasar Birtaniya, da yasa dole gwamnatin kasar ta saka sabbin dokoki na kiyaye yaduwarta da suka hada da dokar shiga da fice da balaguro a fadin kasar.

Farfesa Christian Happi, ya ce an gano wannan nau’i na Korona ne a gwajin jinin wasu mutum biyu da aka yi wa gwajin Korona. Daga nan ne aka gano cewa tasu Koronan sabuwa ce ba ta da din bace.

Sai dai kuma ba a tabbatar cewa ko wannan nau’i na korona ce yasa ake ta samun karuwar yawan wadanda suke kamuwa da cutar akasar nan yanzu.

Farfesa Happi ya bayyana wa PREMIUM TIMES a hira da yayi ta ita cewa ba zai iya battabar da ko sabuwar Koronar bace take yaduwa kamar wutar daji a kasar nan saboda an gano ta tun a watan Oktoba ne, wanda a lokacin ba a samu yaduwar ba kamar yadda ake samu yanzu.

” Yanzu dai akwai yiwuwar kila a samu karin wadanda suka kamu da cutar ta sanadiyyar wannan sabon nau’i na Korona. Amma dai sai an yi gwaje-gwaje tukunna.

Shugaban hukumar NCDC Chikwe Iheakweazu ya bayyana cewa a yanzu dai suna jiran shawarar hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO game da wannan nau’i na Korona. Sannan kuma da maida hankali wajen ganin an ci gaba da kiyaye dokokin korona musamman ga matafiya da kuma mutane baki daya.

Sannan kuma, gwamnati ta yi kira ga mutane ci gaba da bin dokokin samar da kariya daga kamuwa da cutar sannan ta hanyar saka takunkumin fuska, yin nesa-nesa da juna da kuma kula da lafiyar jiki.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button