Ciwon Lafiya

Anyi wa sarkin Hadejia, Adamu Abubakar-Maje allurar rigakafin Korona

Maimartaba sarkin Hadejia, Adamu Abubakar-Maje ya yi allurar riga-kafin korona a babbar asibitin garin Hadejia a ranar litinin.

Sarkin Hadejia wadda shi ne shugaban sarakunan Jihar Jigawa ya zama mutum na biyu cikin masu fada a ji a jihar da aka yi wa allurar rigakafin korona bayan gwamna Muhammadu Badaru.

Mai magana da yawun masarautar ta Hadejia Muhammed Talaki, yace sarkin ya samu tarba daga shugaban asibitin na Hadejia Abdullahi Namadi da sauran Jama’a.

Sarkin yabi duk ka’idojin da ake bi kafin ayi masa rigakafin, inji Talaki.

Sarki Abubakar-Maje yayi addu’a ga Allah ya kawo karshen annobar Korona da kuma rashin tsaro da kasa take fama da ita.

Sarkin ya samu rakiyar manya manyan masu riko da sarautun gargajiya na kasar Hadejia irinsu Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdul’aziz, Wazirin Hadejia Alhaji Hashimu Amar, Iyan Hadejia Alhaji Abdulkadir Abubakar-Maje

Saura sun hada da Sarkin Fulanin Hadejia Alhaji Abubakar Usman da kuma sakataren masarautar Hadejia, Alhaji Baffale Abbas wadanda duk suma anyi musu allurar rigakafin ta korona.


Source link

Related Articles

109 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button