Labarai

Ba a saki fasinjojin jirgin kasan Kaduna dake tsare hannun ƴan bindiga ba

‘Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tun a watan Maris sun ce har yanzu ba a sako ‘yan uwan su ba.

‘Yan uwan sun fadi haka ne bayan labarin cewa wai ‘yan bindigan sun sako fasinjojin ya kareda shafukan sada zumunta a yanar gizo.

PREMIUM TIMES ta samu bayanin haka ne a wani takarda da shugabannin kungiyar ‘Relatives of AK9’ AbdulFatai Jimoh da Ba’aba Muhammad suka fitar ranar Alhamis a garin Kaduna.

Muna kira ga mutane da su yi watsi da labarin wai an sako waɗanda ƴan bindiga suka sace a jirgin kasa na Abuja-Kaduna. Wannan labari karya ne kawai.”

Wata cikin ‘yan uwan fasinjojin jirgin dake tsare hannun ƴan bindigan da aka yi garkuwa da su mai suna Habiba Dalhat ta ce wannan magana ba gaskiya ba ne.

“Muma haka muka samu labarin wai an sako ‘yan uwan mu, amma kuma ba haka bane.

Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan bindiga suka tada na nakiyar da suka dasa a layin dogon jirgin kasan Abuja-Kaduna inda suka kashe mutum 9 sannan suka yi garkuwa da mutane da dama.

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewa tana kokarin ganin an sako fasinjojin sai dai bayan kwanaki 70 mutum biyu ne kadai aka saki. Shugaban bankin manoma Alwan Hassan da wata mata mai ciki aka saki.


Source link

Related Articles

One Comment

  1. you are really a just right webmaster. The site loading
    speed is incredible. It kind of feels that you’re doing any distinctive trick.
    Moreover, The contents are masterwork. you’ve performed a wonderful activity on this subject!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news