KannyWood

BA DON AFAKALLAHU BA, DA YANZU KANNYWOOD TA ZAMA TARIHI: Kashi na 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga ALIYU A. GORA II
A matsayi na na dan jaridar da ya dade ana fafatawa da shi a masana’antar finafinan Hausa, na sha rubuce-rubuce, musamman dangane da makomar Kannywood a mahangar Kimiyyar zamani. Duk da ya ke a baya, ‘yan Fim sun sha fama da kalubale kala-kala, har ta kai ga wasu sana’ar ma ta gagare su kwata-kwata.
Ban mantawa a wancan lokacin, Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano na daya daga cikin manyan matsalolin da su ka janyo wa masana’antar fim tarnaki.

Har na tuna da Malam Rabo, tsohon shugaban Hukumar tace Finafinan da ya lashi takobin ganin bayan harkar fim gaba daya a yankin Arewacin Nijeriya ba ma jihar Kano kawai ba.
Ya yi amfani da kujerar sa wajen fatattakar ‘yan fim daga Kano, inda su ka yi ta hijira zuwa wasu garuruwa domin tsira da mutuncin su. Ya karya ‘yan kasuwar finafinai, ya tura ‘yan Fim da mawaka da marubuta da dama zuwa gidan yari, ciki kuwar da ni kai na.

‘Yan Fim sun sha shirya tarurrukan yin addu’o’in neman mafita daga ukubar da hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta sanya su a wancan lokacin.

Ba zato ba tsammani, Allah ya yi masu gyadar dogo, inda gwamna Ganduje ya zabi daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar finafinan Hausa Isma’il Na’abba Afakallahu a matsayin shugaban Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano mai ci yanzu.

Da yawa sun zuba ruwa kasa sun sha, wasu sun yi yanka saboda murna, wasu sun shirya walima, kasancewar wanda ya san mutuncin su da na sana’ar su ke kan mulki.

Ko tantama babu, Afakallahu ya taka rawar gani fiye da da yadda ake tsammani ta fuskar inganta harkar fim, da kuma kokarin goge bakin fentin da a baya aka goga wa ‘yan fim, da karfi da yaji aka haddasa kiyayya tsakanin su da mutanen gari.

A karkashin jagorancin Afakallahu a hukumar tace finafinai ne ‘yan fim su ka fara samun shiga a harkokin gwamnati, har ta kai ga ana ba wasun su mukamai, ana kuma sauraren shawarwarin su a gwamnatance.

Sai dai kash, daga cikin mutanen da su ka shugabanci hukumar tace finafinai ta jihar Kano, babu wanda ya kai Afakallahu fuskantar kalubale daga abokan sana’ar sa ‘yan fim. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da abin da masu iya magana ke cewa, ‘Ido wa ka raina?’ Ya ce wanda na fi gani kullum.

Ni dai na san a tarihin Kannywood, ba a taba samun lokacin da ‘yan fim su ka samu mahaukatan kudi kamar zamanin Afakallahu a hukumar tace finafinan Hausa ta jihar Kano ba.
An ce idan ba ka san gari ba saurari daka. Don haka mai karatu ka biyo ni bashin hujjojin da na dogara da su cewa, ‘Ba Don Afakallahu Ba’, da yanzu Kannywood ta zama Tarihi.

Mu hadu a rubutu na gaba…

Bissalam


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button