Labarai

Ba gaskiya ba ne wai za a doɗe hanyoyin sadarwa a Jihar Kaduna – Gwamnatin Kaduna

Kakakin gwamnan jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye ya ƙaryata raɗeraɗin da yai yaɗawa a yanar gizo da wasu kafafen yaɗa labarai cewa wai hukumar NCC za ta doɗe hanyoyin sadarwa a jihar saboda tsaro.

Adekeye a madadin gwamnatin jihar ya ƙaryata wannan labari inda ya kara da cewa babu irin wannan magana kwatakwata.

” Gwamnatin Kaduna bata kai kukan abu mai kama da irin haka ba ga wata hukumar gwamnatin tarayya domin a doɗe hanyoyin sadarwar Kaduna ba. Idan har irin haka ma ya zama dole gwamnati ba zata yi boyeboye za ta sanarwa mutanen jihar kai tsaye.

” Wasu ne da ba su kishin jihar suke kirkiro wannan magana sannan suka tambarin jihar domin  su kawo ruɗani a tsakanin jama’ar jihar.

Gwamnati ta ce idan bukatar hakan ma ya taso ba za ta yi kasa-kasa ba wajen bin hanyoyin da ya dacewa sannan kuma za a sanar wa jama’a a sahihan shafukan watsa labaran jihar dauke da saka hannayen mahukunta.


Source link

Related Articles

11 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button