Labarai

Ba kuɗaɗe na rore na yi niyyar gudu ba, hanzarin ganin likita ya sa na yi ƙoƙarin tafiya Amurka ranar da na sauka -Willie Obiano

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano ya musanta raɗe-raɗin cewa EFCC ta kama shi ranar da ya sauka daga mulki, lokacin da ya ke ƙoƙarin tserewa zuwa birnin Houston, Jihar Texas ta Amurka.

EFCC ta damƙe Obiano a Babban Filin Jirgin Legas ya na daf da shiga jirgi zuwa Houston a ranar 17 Ga Maris, jim kaɗan bayan ya sauka mulki.

An maida shi Hedikwatar EFCC a ranar 18 Ga Maris, inda ya kwashe sati ɗaya a kulle kafin a bayar da belin sa.

A tattaunawa da lauyan Obiano mai suna Patrick Ikwuetor, ya ce tsohon gwaman ya yi niyyar garzayawa Amurka ne domin ganin likitan sa da gaggawa inda ya ke zuwa duk bayan watanni uku aka yi masa gwaji da binciken matsalolin da suka shafi ɓangaren mafitsa.

Ikwuetor ya ce Obiano ya yi sa’a an gano matsalar sa tun kafin ta kai ga muni. Shi ya sa tun a cikin watan Yuni, 2021 ake masa bincike da gwaje-gwaje da gashi duk bayan watanni uku.

“Ta yaya Obiano zai gudu a ranar da ya kammala mulkin sa? Ta ya zai gudu alhali ga iyalan sa a nan Najeriya?

“Likitoci sun ce za a yi masa gwaje-gwaje cikin gaggawa kuma a yi masa aiki tare da kwantar da shi ana yi masa gashi har tsawon makonni takwas ”

Lauyan bai shaida wa wakilin mu ainihin ciwon da ke damun Obiano ba. Sai dai kuma wata majiya ta shaida mana cewa Obiano ya san EFCC ta na bin sa tun cikin 2021. Kan haka ne ma a cewar lauyan sa, kafin ya yi niyyar fita sai da Obiano ya tuntuɓi janmi’an gwamnati, ya tabbatar masu idan ya je Amurka, zai dawo.

Wata majiya ta ce Obiano ya tuntuɓi Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda Hukumar EFCC ke ƙarƙashin sa. An ce Malami ya ce masa zai sa EFCC su ɓalle dabaibayin da suka garƙama masa, sai ya dawo a ci gaba da bincike. Amma hakan bai hana EFCC damƙe shi ba.

Premium Times Hausa ta buga labarin cewa sabon Gwamnan Anambra Charles Soludo ya ce, ‘naira miliyan 300 kaɗai Obiano ya bari a Asusun Gwamnantin Anambra, sai tulin bashin naira biliyan 109.’

Sabon Gwamnan Jihar Anambra, wanda aka rantsar cikin makon da ya gabata, Charles Soludo ya ce ya ci gadon naira miliyan 300 kaɗai daga gwamnatin Obiano, wanda ya sauka makon jiya.

Da ya ke bayani a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin safe na Gidan Talabijin na Arise a ranar Laraba, Soludo ya ce an bar kuɗi cikin cokalin da ba su wuce naira miliyan 300 zuwa 400 ba, amma kuma tulin bashin da gwamnatin da ta sauka ta bari ya kai Naira biliyan 109.

Ya ce amma wannan ba zai sare masa guyawu ba, zai yi aiki tuƙuru domin bunƙasa jihar Anambra, duk kuwa da cewa asusun jihar babu komai a ciki.

“Kuɗin da mu ka taras ba su wuce Naira miliyan 300 zuwa miliyan 400 ba. Sai kuma tulin bashin da ya zuwa ranar 31 Ga Disamba, 2021 bashin da ake bin Anambra ya kai Naira biliyan 109.” Inji Soludo.

Daga nan ya ce zai bunƙasa jihar ta hanyar maida hankali kan amfani da kayan cikin gida, maimakon na ƙasashen waje.

Ya ce bai ga dalilin da zai sa a riƙa fifita kayan waje ba, alhali ga na gida.

“Yanzu a ce mutum miliyan 215 na Najeriya duk da yadin da ake yi a nan gida su ke ɗunka sutura, ai da an samu ci gaba sosai. Kuma miliyoyin mutane za su samu aikin yi.”

Premium Times ta buga labarin yadda EFCC ta damƙe Willie Obiano yayin da ya ke shirin tserewa Amurka, bayan an gaggaura wa matar sa mari a wurin da ya damƙa wa Soludo mulki Jihar Anambra.

Jami’an EFCC sun ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano cancak daga ofishin su na Shiyyar Legas zuwa Hedikwatar EFCC ta Abuja domin ci gaba da sharara masa tambayoyin salwantar maƙudan kuɗaɗe a lokacin mulkin sa.

Obiano zai sha tambayoyi bayan kuma an sharara wa matar da Misis Obiano mari a gaban jama’a, yayin da su ke miƙa mulki ga sabon Gwamnan Anambra, Charles Soludo.

EFCC ta kama Obiano a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan ya miƙa mulki a Enugu.

Ya garzaya Legas ne da nufin hawa jirgin sama zuwa Jihar Houston a Amurka, inda jirgi ke jiran sa.

Wannan rana ta zama baƙar rana ga Obiano, wanda a gaban sa kuma a gaban dubban jama’a, Bianca Ojukwu ta gaggaura wa matar sa mari wurin miƙa mulki.

Majiyar EFCC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an damƙe Obiano wajen ƙarfe 8:30 na dare a ranar Laraba, kuma washegari Alhamis aka ɗauko shi a jirgi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

Har yanzu dai ba a san takamaiman ko naira biliyan nawa EFCC ke ƙoƙarin ganin Obiano ya amayas ba.

Sai dai kuma idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labari ƙarshen 2021 cewa Hukumar EFCC ta rubuta wa Hukumar Shige da Fice Wasiƙa a ranar 15 Ga Nuwamba cewa su sa ido kan Obiano duk inda zai fita daga ƙasar nan. Su kula da ranar da zai fita ko ranar dawowar sa.

EFCC ta kama shi sa’o’i kaɗan bayan ya rasa rigar sulken kariya a lokacin ya na gwamna, rigar da ke hana duk irin ɓarnar da gwamna ya yi, ya fi ƙarfin kamu, sai dai a jira bayan saukar sa.


Source link

Related Articles

11 Comments

 1. I really like your blog.. very nice colors & theme. Did
  you design this website yourself or did you hire someone to do
  it for you? Plz reply as I’m looking to create my own blog and would
  like to know where u got this from. thanks a lot

 2. You actually make it appear so easy together with your presentation but I in finding this topic to be actually one thing that I feel I might never understand. It kind of feels too complicated and very wide for me. I’m looking ahead to your next publish, I?¦ll try to get the hold of it!

 3. Woah! I’m really digging the template/theme of this blog. It’s simple, yet effective. A lot of times it’s hard to get that “perfect balance” between user friendliness and appearance. I must say you have done a excellent job with this. In addition, the blog loads extremely fast for me on Firefox. Excellent Blog!

 4. I am not sure the place you are getting your info, but good topic.
  I must spend a while learning more or working out more.

  Thank you for magnificent information I used to be on the lookout for this information for my mission.

 5. Hey I know this is off topic but I was wondering if you knew of any widgets
  I could add to my blog that automatically tweet my newest twitter updates.
  I’ve been looking for a plug-Jobs In Editing And Proofreading like
  this for quite some time and was hoping maybe you would have some
  experience with something like this. Please let me know if you run into
  anything. I truly enjoy reading your blog and I look forward to your new
  updates.

 6. Hey I know this is off topic but I was wondering if you knew
  of any widgets I could add to my blog that automatically tweet
  my newest twitter updates. I’ve been looking for a plug-in like this for
  quite some time and was hoping maybe you would have some experience with something
  like this. Please let me know if you run into anything.

  I truly enjoy reading your blog and I look forward to your new updates.

  Look at my site :: article directory

 7. Someone necessarily lend a hand to make significantly articles I might state. That is the very first time I frequented your website page and to this point? I surprised with the research you made to create this particular post incredible. Magnificent job!

 8. I like the valuable info you provide in your articles.
  I’ll bookmark your weblog and check again here frequently.
  I’m quite certain I will learn many new stuff right here!

  Best of luck for the next!

  Here is my web page … Bookmarks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news