Siyasa

Ba Mu Muka Yi Wa Pantami Ihu Ba Inji Yan Kwankwasiyya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano a Najeriya kuma daya daga cikin masu fada a ji a kungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Bichi ya ce ba mambobin kungiyarsu ba ne suka yi wa ministan sadarwar kasar Ali Isa Pantami ihu a lokacin da ya je birnin Kano.

Hakan na zuwa ne bayan da wani bidiyo ya yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta a ranar Talata, inda aka ga mutane masu sanye da jajayen huluna suna cin mutuncin ministan ta hanyar yi masa ihu a filin jirgin Malam Aminu Kano.

Rabi’u Bichi ya ce “yaranmu masu son zaman lafiya ne saboda haka ba za su tayar da zaune tsaye ba, illa dai kawai abokan hamayyarmu ne da ke son bata mana suna suka yi wannan ihu.

Mu mun je yi wa daliban da za su tafi kasar waje karatu rakiya ne. Saboda haka yaran da suka yi wa ministan ihu ba sa tare da mu. Karewa ma yaran namu ne suka cece shi.”

To sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan filin jirgin na Malam Aminu Kano, DSP Alabi Josoph wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin ya ce ‘yan Kwankwasiyya ne suka yi wa ministan ihu a lokacin da ya je filin jirgin na Kano domin tashi zuwa Abuja.

DSP Alabi ya kara da cewa ‘yan sanda da hadin gwiwar jami’an tsaron filin jirgin saman ne suka kwantar da tarzomar cikin kankanin lokaci.

“Da misalin karfe 2: 30 na ranar 24 ga watan Satumba, ‘yan kungiyar Kwankwassiya sun yi wa ministan sadarwa ihu wanda ya je filin jirgin saman malam Aminu Kano domin tashi zuwa Abuja.

“Ministan ya je filin jirgin a dai-dai lokacin da ‘yan Kwankwasiyya su ma suka je filin jirgin domin yin rakiya ga dalibai kimanin 200 da za su tafi karatu kasar waje. Kuma a nan ne suka yi wa ministan a ture-a-ture har sai da jami’an tsaro suka shiga al’amarin kuma cikin kankanin lokaci kura ta lafa”. In ji DSP Alabi.

Wannan batu dai ya janyo kace-na-ce a kafafen sada zumunta inda wasu suka yi ta sanya bidiyon da ake tunanin shi ne ya janyo takaddama;

BBC ta yi kokarin jin ta bakin ministan Sadarwar, Dr Ali Isa Pantami inda bai dauki kiran waya ba ko kuma yin martani ga sakon wayar hannu da aka aike masa.

Ana dai hasashen cewa rashin jituwa tsakanin minista Pantami da ‘yan Kwankwasiyya ta fara ne a farkon shekarar nan kafin yin babban zabe, inda shi Sheiukh Pantami ya yi wani wa’azi da ‘yan Kwankwasiyyar suka ce ya taba jagoransu, Rabiu Kwankwaso.

Karo na biyu ke nan a baya-bayan nan da wasu jama’a ke yi wa wani mai rike da mukami a gwamnatin Najeriya a ture-a-ture, tun bayan da abun da ya faru da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriyar, sanata Ike Ekweremadu a Jamus a watan da ya gabata.


Source link

Related Articles

15 Comments

  1. 977450 167550Your article is truly informative. Far more than that, it??s engaging, compelling and well-written. I would desire to see even much more of these types of great writing. 835422

  2. 808760 997882Hello there, just became alert to your blog via Google, and located that its really informative. Im gonna watch out for brussels. Ill be grateful should you continue this in future. Many people will probably be benefited from your writing. Cheers! 395698

  3. 51512 36403This is sensible information! Exactly where else will if ind out much more?? Who runs this joint too? sustain the good work 155148

  4. 806581 994488Beneficial information and outstanding style you got here! I want to thank you for sharing your ideas and putting the time into the stuff you publish! Excellent function! 11791

  5. What¦s Taking place i’m new to this, I stumbled upon this I have discovered It positively useful and it has helped me out loads. I hope to give a contribution & assist other users like its aided me. Good job.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button