KannyWood

Ba Muneerat Abdulsalam Ya Kamata A Nema Wa Kudi Domin Ta Sauya Sana`a Ba

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Ibrahim Bello (Irosis)

A jiya Talata 10 November, 2020 daya daga cikin manyan marubutanmu na Arewa kuma mamallakin jaridar Mikiya wato Muhammad Inuwa Hamisu wanda aka fi sani da M Inuwa MH, ya yi wani rubutu a kan cewa zai shige gaba wajen nemawa muneerat Abdulsalam taimakon makudan kudade Miliyoyi daga ‘yan uwa masu kishin Addinin islama a matsayin kudin jarin da za ta canja sana’arta matukar da gaske take domin Addinin islama bai aminta da sana’ar da take yi ba a matsayinta na Musilma.

Inda ya bayyana cewa zai kira Muneerat su yi magana idan ta aminta za a fara neman gudunmawar makudan kudaden. Bayan sun yi magana da ita kuma ta aminta sai ya wallafa a shafinsa da misalin karfe 10pm na dare, inda ya saka lambar asusun ajiya na kamfaninsa Mikiya domin fara neman gudunmawar.

Alhamdulillah abin da M Inuwa MH ya zo da shi tunani ne mai kyau, domin duk musulmin kwarai ba zai so ganin Muneerat Abdulsalam tana wannan sana’ar ba kuma tana da’awar ita musulma ce, muna godiya da nuna kishinka a kan addinin musulunci. Sai dai abubuwan lura a nan su ne:

1) Muna da marasa lafiya a Arewa wadanda suke bukatar taimako don ceto rayuwarsu, domin wasu a kan kudi kalilan rayuwarsu take salwanta.

2) Arewa akwai gajiyayyu da suke bukatar tallafi domin su samu abin da za su cigaba da rayuwa, tun kafin yanayin rayuwa ya sa su tsinci kansu a cikin bara.

3) Akwai ‘Yan gudun hijira birjik a Arewa wadanda suka fi Muneerat Abdulsalam bukatar taimako ta kowane fanni a rayuwa.

4) Har ila yau a Arewa muna da Marayu da suke da bukatar agaji sosai fiye da Muneerat Abdulsalam.

5) Muna da talakawa da yawa a Arewa wadanda suka fi Muneerat Abdulsalam bukatar jari domin su dogara da kansu.

Wadannan da ma wasu dalilan ya sa nake ganin kamar ba Muneerat Abdulsalam ce yafi cancanta da a nemawa wannan kudade ba, kamata ya yi a nema ma wadanda suka fita bukata domin a tallafa ma rayuwarsu.

Na san wasu za su ce, suna ganin rubutun nema wa gajiyayyu da marasa lafiya taimako daga shafin Jaridar Mikiya, Rariya, Dokin Karfe da dai sauransu, tabbas suna yin irin wannan rubutu kuma muna yaba ma kokarinsu a kan hakan.

Amma babban makasudin kawo wadannan dalilai shi ne, ita dai Muneerat Abdulsalam ko a yanzu mai kudi ce a karin kanta, don haka za ta iya amfani da kudinta ta sauya daga sana’ar da take yi zuwa kowace irin sana’a take ra’ayi wacce musulunci ya aminta da ita, don haka ba sai an tara makudan kudi an mallaka mata ba, alhali akwai mutanen da suka fita bukata.

Allah Ya bamu ikon taimakawa, Allah Ya zaunar da kasarmu Najeriya lafiya. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.


Source link

Related Articles

47 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button